1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janar al-Burhan ya tsige Daglo daga mataimakinsa

Binta Aliyu Zurmi
May 20, 2023

Janar Abdel Fattah al-Burhan ya tsige mataimakinshi kuma abokin gabarsa Mohammad Hamdan Daglo daga mataimakin shugaban rikon kwarya kasar Sudan.

Sudan |  Abdel Fattah Abdelrahman al-Burhan
Hoto: Mahmoud Hjaj /AA/picture alliance

Wannan sanarwar na zuwa ne a yayin da dakarun RSF da na sojojin gwamnati ke ci gaba da gwabza kazamin fada a birnin Khartoum da ma yankin Darfur.

Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta UNCHR na gargadin rashin kawo karshen wannan fada na kara yawan mutanen da ke buukatar agajin gagawa a kasar da yaki ya barke tun a tsakiyar watan Afirilu.

A cewar Martin Griffiths jami'in MDD mai kula da ayyukan jinkai, ya ce yanzu haka sun sake samar da dalar Amurka miliyan 22 domin taimakawa 'yan sudan da ke tserewa yaki.

Ko a jiya Juma'a masu aiko da rahotanni sun tabbatar da barin wuta a tsakanin bangarorin biyu, inda aka ce a yankin darfur fadan ya rikide ya zuwa na kabilanci a tsakanin fararen hula wanda tuni ya yi asarar gwamman rayuka.