1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janar Babacar Gaye ya fara jagorantar sanya idanu a rikicin Siriya

July 26, 2012

Mazon da Majalisar Ɗinkin Duniya ta aike Siriya domin jagorantar dakarunta wajen sanya idanu kan halin da ƙasar ke ciki wato Janar Babacar Gaye ya isa Siriyan domin kama aiki.

epa03224209 Moroccan Colonel Ahmed Himmiche (R) of the United Nations observers mission in Syria receives Babacar Gaye (L) military adviser to UN Secretary Ban Ki-moon, in Damascus, Syria, 18 May 2012. The chief of United Nations military observers in Syria Major General Robert Mood said on 18 May violence has increased this week in the country despite the increasing number of observers deployed to monitor the ceasefire. EPA/STR +++(c) dpa - Bildfunk+++
General Babacar GayeHoto: picture-alliance/dpa

Janar ɗin wanda ɗan asalin kasar Senegal ne zai jagoranci tawagar soji ɗari da hamsin domin gudanar da aiyyukan sanya idanu na tsawon kwanaki talatin bayan da kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya tsawaita wa'adin aikin dakarun da ke sayan idanu kan rikicin na Siriya.

Cigaba da aikin na dakarun na Majalisar Ɗinkin Duniya dai na zuwa ne daidai lokacin da ake cigaba da gwabza faɗa tsakanin dakarun gwamnatin ƙasar da masu rajin kawo sauyi.

Masu aiko da rahotanni dai na cewar dakarun ɓangarorin biyu na ƙara yawan mutanensu a garin Aleppo da kuma Damuscas, fadar gwamnatin ƙasar a wani yunƙuri na karɓe iko da yankunan.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Umaru Aliyu