Tsohon janar din Najeriya ya rasu a hannun 'yan bindiga
June 13, 2026
Talla
Rahotanni sun ce marigayin ya rasu ne bayan ya shafe wani lokaci a hannun masu garkuwa da mutanen da suka sace shi tare da matarsa a wani hari da suka kai a jihar.
Mutuwar tasa ta girgiza al’umma da dama, musamman duba da irin gudunmawar da ya bayar wajen kare kasa a lokacin da yake aiki a rundunar sojin Najeriya.
Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana alhininta kan wannan lamari, inda ta lashi takobin daukar matakan da suka dace na ganin sun karbo gawarsa da mai dakinsa da suke ci gaba da zama a hannun 'yan bindiga.