1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sabon jagoran mulkin soji ya bayyana

Abdourahamane Hassane
July 28, 2023

Bayan an kwashe kwanaki ana yin tababa dangane da makomar wanda ya yi juyin mulki a Nijar,a karon farko Janar Abdourahamane Tchiani ya bayyana a gidan Talbijan na Nijar a mastsayin sabon shugaba.

Janar  Abdourahamane Tchiani Jagoran mulkin soji na Nijar
Janar Abdourahamane Tchiani Jagoran mulkin soji na NijarHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

A karon farko tun bayan juyin mulkin da ya yi sabon jagoran mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tchiani ya yi jawabi a gidan telbijan da rediyo na kasar inda ya bayana dalilan da ya sa suka yi juyin mulki.''Ya ku 'yan kasa 'yan Nijar a ranar Larba hadin gwiwar sojojij na kwamitin CSNP na ceton kasa ya kawo karshen mulkin Jamhuriyar ta bakwai domin ceton kasarmu, saboda rashin gudanar da kyakyawan mulki da gwamnatin Jamhuriyar ta bakwai ta yi da almubazaranci da dukiyyar kasa, sannan ga rashin tsaro da ya adabi kasarmu.''Yanzu haka dai sojojin na Nijar na ci gaba da tsare tsohon shugaban Mohammed Bazum a gidansa tare da iyalansa, sai dai Bazoum din yana yin turjiya a kan juyin mulkin.