1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janye makamai daga iyakar kasashen Koriya

Gazali Abdou Tasawa
October 16, 2018

A ci gaba da kokarin da kasashen Koriya ta Arewa da ta Kudu suke yi na neman sansanta junansu, wasu tawagogin jami'an gwamnatocin kasashen biyu na taro kan iyakar kasashen biyu kan batun janye makamai daga iyaka.

Nord- und Südkorea vereinbaren Entspannungsschritte (Symbolbild)
Hoto: Getty Images/South Korean Unification Ministry

A ci gaba da kokarin da kasashen Koriya ta Arewa da ta Kudu suke yi na neman sansanta junansu, wasu tawagogin jami'an gwamnatocin kasashen biyu sun soma a wannan Talata a bisa sa idon wasu jami'an Majalisar Dinkin Duniya da kasar Amirka, wani zaman tattaunawa kan batun kunce damarar yaki a yankin Punmunjon na kan iyakar kasashen biyu inda kowacensu ta jibge tarin makaman yaki da sojoji a karshen yakin da suka gobza daga shekara ta 1950 zuwa 1953. 

A karkashin shirin sansantawar dai tuni kasashen biyu suka fara aikin tone nakiyoyin da suka dasa a yankin na Panmunjon inda a baya bayan nan kasashen biyu ke yawan gudanar da tarukan hadin gwiwa. 

Kazalika shirin ya tanadi janye na'u'rorin sa ido da kasashen biyu suka girke da zaran an kammala aikin kunce nakiyoyin. Bugu da kari shugabannin kasashen biyu sun sha alwashin janye shingayen tsaro na kan iyaka da kuma dakatar da gudanar da atisayen sojoji a yankin daga watan Nowamba mai zuwa.