1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Janye tallafin lantarki a Najeriya

February 3, 2026

A wani abun da ke iya jefa daukacin masana'antar wuta a tarayyar najeriya cikin rudani, gwamnatin kasar ta ce tana shirin kare daukar nauyi na tallafin wutar kasar a ita kadai.

Wutar lantarki a Najeriya
Wutar lantarki a NajeriyaHoto: Akintunde Akinleye/REUTERS

Miliyoyi na yan kasar a karkara dai na samun sauki cikin farashi na wutar sakamakon tsarina farashin da ya mai da kai a birane na kasar. Ya zuwa yanzun dai akalla Naira Triliyan biyu ne Abuja ta ce tana biya a shekara a kokari na sauke farashi cikin wutar da 'yan kasar ke da bukata.

Dalilin gwamnatin

Wutar lantarki a NajeriyaHoto: Akintunde Akinleye/REUTERS

To sai dai kuma tun daga shekarar bana dai Abuja ta ce nauyin na kara yawa, kuma tana bukatar ta rage a kokarin daidaito cikin batun kudi. Daga yanzu kuma a fadar ofishin da ke tsarin kasafin kudin kasar, gwamnatin kasar tana shirin raba tallafin da jihohin kasar da ke bukatar sauki cikin wutar da al'ummarsu ke sha.

Sabo na matakin dai daga dukka na alamu na shirin kara yawan kudin wutar tsakanin miliyoyin al'ummar dake a kauyuka da karkarar tarayyar Najeriyar a halin yanzu. Can cikin tsari dai haske na wutar yana zama daya tilo da gwamnatin take da tallafawa yan kasar a kansa, bayan zare tallafin harkar mai da kau da kai cikin harkar noma.

Wutar lantarki a Najeriya da sauyin makamashiHoto: Jet Motors/(Xinhua /picture alliance

Sannu a hankali dai Najeriyar a karkashi na gwamnatin ta Tinubu na ta adabo da tallafi iri iri tsakanin al'umma. Ba kuma tare da inganta rayuwar ma#aikata da kila ma ragowar al'umma ba. A yayin da farashin na wuta yake kara sama, albashin 'yan kasar yana zaman na kurar baya a daukacin yankin yammacin Afrika a yanzu. Yusha'u Aliyu dai kwarrare ne ga tattali na arzikin da kuma yace batun na tallafi yana zaman ruwan dare game duniya.

Akwai dai tsoron zare tallafin a kauyuka na iya shafar tattalin arziki a karkarar. Miliyoyin kananan sana'o'in dai na dogaro kan harkar ta wuta a kokari na rayuwa da ci-gaban al'umma.