1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan kwadago sun tsayar da gangami

August 3, 2023

Kasa da tsawon awoyi 24 da fara wata zanga-zanga bisa zare tallafin man fetur, masu kwadagon Najeriya sun ayyana janye zanga-zangar da ke da babban burin sauyi.

Nigeria Protest NLC Abuja
Masu zanga-zangar neman sauyi a AbujaHoto: Uwais/DW

Akasin abun da ke zaman al'ada, wata sanarwa daga fadar gwamnatin kasar ce ta kai ga kare zanga-zangar da ke zaman irinta ta farko ga sabuwa ta gwamnatin.

Wata ganawa a tsakanin manya na jami'ai na kungiyar ta kwadagon da shugaban taraiyar Najeriya, daga dukka na alamu ce ta kai ga sauyin lamura tare da sauke masu kwadagon  tashi daga dokin rikicin da ya tada hankalin yan mulki na kasar.

Joe Ajero dai na zaman  shugaba na kungiyar NLC da kuma yayi tsaiwa irin ta gwamen jaki bayan ganawa da shugaban kasar bisa hujja ta janye zanga-zangar da karuwa ta azaba ta zare tallafin a halin yanzu.

"Eh lallai mun gana da shugaban kasa, kuma batutuwan da muka tattauna sune dai batutuwan da suka kaimu ga zanga-zangar. Kuma ya fadi matsayinsa, kuma ya dau alkawari kamar yadda muka gani a majalisun taraiya.

Hoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Kuma zamu koma ya zuwa ga mutanen mu domin nazari. Abubuwan da ya fada a jawabinsa na 'yan kasa suna da daman gaske, amma kuma akwai batu guda daya zuwa biyu da ke bukatar kallon natsuwa. Kuma shugaban kasa dan fafutukar 'yanci ne saboda haka yasan muhimmanci na zanga zanga."

'Yanci na zanga-zanga ko kuma kokarin biya na bukata dai,  masu kodagon kasar dai sun ce gwamnatin kasar tai musu alkawarin gyara na matatar man kasar mafi tasiri ta fatakwal kafin karshe na shekarar bana. Sake mai da aiki na matatun dai na zaman daya a cikin alkawuran da ke tsakani na gwamnatin Najeriyar da masu kwadagon kafin kaiwa ga zare tallafin man fetur.

To sai dai kuma sannu a hankali matatun na neman komawa kafa ta satar biro, maimakon rage farashin man da kila samun sauki ga 'yan kasa. Engineer Zailani Mohammed dai na zaman tsohon jami'i a kamfanin mai na kasar da kuma yace ko babu fatakwwal akwai dabarun sauki ga yan kasar cikin sabon tsari na kamfanin NNPC .

Masu zanga-zangar neman sauyi a KanoHoto: Nasir Salisu Zango

To sai dai in har sabuwa ta gwamnatin tana shirin matse ruwa daga dutsen rashawar da ta dauki lokaci tana ta mamaya a harka ta matatun, majiyoyi   na masu kodagon dai sun ce ma'aikata na gwamnatin tarrayar  sun nasarar karbar kusan kaso 40 cikin dari na albashinsu da shugaban kasar ya bada umarnin a biya nan take.

Dama dai an  dade ana zargi na masu kwadagon da daukar jama'ar gari cikin ruwa sannan kuma su tsallake zuwa ga bukata to sai dai kuma a tunanin Comrade Mohammed Tahir dake a zaman shugaban kungiyar dillallan dabbobbi da abinci,  matakin NLC na zaman kokari na ja da bayan rago.

Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa a tsakanin jama'ar cikin garin dake bukatar sauki, da masu kodagon dake kallon dama a cikin rikicin na zare tallafi.