1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Janyewar Amurka daga WHO zai yi illa ga Afirka - CDC

January 23, 2025

Shugaban Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afirka (Africa CDC) ya ce matakin na shugaba Donald Trump zai yi gagarumin tasiri ga tsare-tsaren kiwon lafiya a nahiyar.

John Nkengasong | Director of the Africa Centers for Disease Control and Prevention
Hoto: Mulugeta Ayene/AP/picture alliance

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afirka (Africa CDC) ta sanar da cewa matakin da shugaba Donald Trump ya dauka na janye Amurka daga cikin Hukumar Lafiya ta Duniya WHO zai yi matukar tasiri ga tsare-tsaren kiwon lafiyar al'umma a nahiyar.

Karin bayani: AU ta nuna damuwarta kan matakin Amurka na ficewa daga WHO

Shugaban Hukumar ta Africa CDC Ngashi Ngongo ya ce wannan mataki mai matukar hadari ga Afirka ya zo musu da ba zata, kuma zai haifar da raguwar kashi 10 cikin 100 na kudaden gudarwar Hukumar.  

A daura guda kuma mista Ngongo ya ce janyewar ta Amurka za ta shafi kai tsaye kasashe membobin Hukumar WHO, yana mai jaddada cewa kasashen Afirka da dama na samun kudade daga Washington domin yaki da cutuka da dama musamman cutar HIV mai karya garkuwar jiki.

Sai dai da aka tambaye shi ko kasashe irin su China za su iya maye wannan gurbi na Amurka, M. Ngongo ya ce ya kamata hukumar ta Africa CDC ta mika kokon bara ga kasashe masu kekkawar niya da za su iya shigowa domin tallafawa nahiyar.