Japan da Australia sun sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro
March 13, 2007Talla
Kasashen Japan da Australia sun sanya hannu kann wata muhimmiyar yarjejeniyar tsaro tare da nufin samarda zaman lafiya a yankin Asiya Pacific.
Wannan shine karo na farko da kasar Japan ta sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro da wata kasa wadda ba Amurka ba.
Firaministan japan Shinzo Abe wanda ya rattaba hannu tsakanisa da takwaransa da Australia John Howard yace yarjejeniyar ba ta da alaka da batun bunkasa sojojin kasar China ba.
Karkashin yarjejeniyar kasashen biyu zasu hada kai a fannonin wanzar da zaman lafiya,yaki da tarzoma da taimako game da abkuwar annoba ko balai.