1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan na neman Mdd ta kakabawa Koriya tarewa takunkumi

July 9, 2006

Japan

Japan tace zata tursasawa mdd kakabawa koriya ta arewa takunkumi dangane da gwajin makaminta mai linzami.Kasashen Amurka da Britania da faransa dai na marawa japan baya a wannan yunkuri nata,amma kasar Sin na adawa da hakan.A ranar larabar data gabata kadai dai koriya ta arewan ta kaddamar da gwajin makamai masu linzami guda 7,daga cikinsu kuwa harda mai dogon zango da kwararru sukace zai iya kaiwa Alaska,wanda kuma batayi gwajinsa ba.To sai dai a halin da ake ciki yanzu naurar lalata makamai masu linzami na zamani,mallakar sojin ruwa na Amurka ,ya iso kasar sansanin Tokyo dake Japan.