Japan ta kammalla kwasar sojojin ta daga Irak
July 17, 2006ƙasar Japon ta kammalla kwassar sojojin ta daga Iraki.
A yayin da ya ke bayyani da yan jarida, bayan taron G8, Praminista Yunichiro Koizumni, ya ce Sojojin Japon, su kammalla aikin su a ƙasar ta Iraki, cikin sannin ta kamata, ba tare da sun harbi ko ɗan tsako ba.
Ranar 20 ga watan da ya gabata ne, Japon ta umurci sojojin ta 600, su hito daga Iraki.
A ci gaba da hare haren ƙunar baƙin wake kuwa a ƙasar , mutane kussan 50 su ka rasa rayuka, wasu kuma fiye da 40 su ka ji raunuka a yinin yau.
Mace macen , sun abku, a a sakamakon harin da wasu mutane, ɗauke da makamai su ka kai, cikin kasuwar Mahmudiyah, da ke tazara kilomita 30 a kudancin Bagadaza.
Birnin Muhamadiyah na cikin yankin da a ka raɗawa suna zirin mutuwa, ta la´akari da haren haren da ya ke fuskanta lokaci, zuwa lokaci.