1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Halitta da Muhalli

Japan: Komawa kamun babban kifin Whale

Gazali Abdou Tasawa
December 26, 2018

Kasar Japan ta sanar da shirinta na komawa sana'ar kamun babbankin nan da aka fi sani da dabbar Whale wacce dokar kasa da kasa ta haramta.

Japan Symbolbild Walfang
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/Kyodo News

Wannan mataki da kasar Japan ta dauka na komawa kamun wannan kifi da aka fi sani da suna dabbar Whale da Turancin Ingilishi ko kuma baleine a Turancin Faransance shekaru 30 bayan dakatar da wannan sana'a, na matsayin kalubalantar masu fafutukar kare wannan nau'in kifi a duniya. 

Dama dai Shekaru da dama ke nan da kasar ta Japan ke fakewa da hujjar binciken kimiyya wanda wani sashen dokar haramta kamun wannan kifi ya tanada, domin ci gaba da kamun dabbar Whale din.A wannan karon dai ta fito fili ta sanar da bin sahun wasu kasashen kamar Island da Norway wajen komawa sana'ar kamun wannan babban kifi da ke zama mafi girma a duniya.