Japan za ta taimaka wa yankin Sahel na Afirka
June 2, 2013Kasar Japan ta bayyana cewa za ta ba da Euro bilyan guda, domin tabbatar da inganta lamura cikin yankin Sahel na Afirka, watanni bayan hallaka 'yan Japan 10 cikin wani harin 'yan ta'adda masu nasaba da masu kaifin kishin Islama a kasar Aljeriya.
Kudin yana cikin Euro bilyan 14 da kasar za ta bayar na taimakon raya kasa cikin shekaru biyar masu zuwa. Firaministan kasar ta Japan, Shinzo Abe ya bayyana haka yayin taron hadin-gwiwar Japan da nahiyar Afirka, da ke gudana a birnin Yokohama na kasar Japan..
Kasar ta Japan ta bayyana shirin bayar da kudade kimanin Dala bilyan 32, da za a yi amfani da su wajen raya kasa cikin kasashen Afirka.Shinzo Abe ya tabbatar haka yayin taro kan ci-gabar nahiyar. Za a yi amfani da kudade wajen samar da kayayyakin aiki da horar da matasa. Shirin ya hada da bai wa kimanin matasa 1000 damar zuwa kasar ta Japan, domin karatu cikin jami'o'in kasar, da aiyukan samun horo a kamfanonin kasar.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas