Japan zata hada kai da Turkiya don magance yaduwar murar tsuntsaye
January 10, 2006Japan ta ce kofa a bude take wajen hada kai da Turkiya don yaki da yaduwar masassarar tsuntsaye, inji FM Junichiro Koizumi wanda a yau talata ya fara wata ziyarar aiki ta yini 4 a Turkiya. Mun yi musayar ra´ayoyi akan wannan batu, inji FM Koizumi a lokacin wani taron manema labarai na hadin guiwa da suka yi da FM Turkiya Recep Tayyip Erdogan. Koizumi ya ce wannan batu ya shafi duniya baki daya, a saboda haka ministocin kiwon lafiya na kasashen biyu zasu shawarta game da ba juna hadin kai don yakar cutar ta murar tsuntsaye. Rahotannin sun tabbatar da cewa mutane 15 ne a Turkiya suka kamu da kwayoyin nau´in zazzabin tsuntsaye na H5N1 mai mummunan hadari ga bil Adama. A ckin makon jiya mutane yara biyu suka mutu dukkan su ´yan gida daya suka mutu a gabashin Turkiya sakamakon nau´in na H5N1. A wani labarin kuma FM Turkiya Recep Erdogan ya ce an shawo kan yaduwar cutar a cikin kasar sannan ana ci-gaba da yiwa mutanen da suka harbu da kwayoyin H5N1 din kuma ba sa cikin wani mummunan hali.