1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridar Bild ta bukaci sakin 'yan jaridunta a Iran

November 21, 2010

Shugaban jaridar ya ce su ma'akatansan na cikin hali mawuyaci a tsare

Jaridar Bild da ake wallafawa ranakun Lahadi a nan Jamus, ta yi kira ga hukumomin Iran da su saki 'yan jaridanta biyu da ke tsare a wannan ƙasar. Babban editan fitacciyyar jaridar Walter Mayer ya wallafa a shafinta na farko cewar, ɗan jaridar da mai ɗaukar hoton na tsare ne a cikin wani mummunan yanayi. A watan Oktoban da ya gabata ne dai aka cafke 'yan jaridar biyu, a lokacin da suke hira da ɗan wata mata da ta samu tsira da hukuncin kisa ta hanyar jifa. Da farko dai an zargi 'yan jaridar da rashin mallakar takardun izinin tafiyar da ayyukansu a cikin Iran. Tun a ranar ´Juma'a ne dai ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, ya yi kira ga hukumomin Iran da su daraja dokar ƙasa da ƙasa wajen bawa 'yan jaridar damar ganawa da lauya, tare da ba su kulawar da ta kamata a inda suke tsare.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita : Mohammad Nasir Awal