1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jaridun Jamus: 06.09.2024

Usman Shehu Usman AH
September 6, 2024

Huldar China da Afirka da kokarin Jamus na samun makamashi daga Namibiya na daga cikin batutuwan da jaridun Jamus suka ambato.

Hoto: Andy Wong/AP/picture alliance

Sharhunan jaridun Jamus na wannan mako za mu fara ne huldar China da Afirka, inda jaridar die Tageszeitung ta ce China ta kasance babbar kawar Afirka da babu kamarta, kuma ana ci gaba da zurfafa wannan huldar. Nahiyar Afirka da China sune mafiya yawan al'umma a duniya kuma nahiyoyi masu cike da arziki. Bisa wannan ne ya sa China da Afirka suke baji kolin arzikin da Allah ya hore musu, kamar yadda aka gani a taron kwanaki uku na China, taron da ya samu halartar kusan dukkan shugabannin kasashen Afirka. Jaridar ta ce taron nasu bai tashi a banza  ba,saboda  shugaban kasar China Xi Jinping ya sanar da zuba jari na biliyoyin kudi a nahiyar ta Afirka.

Hoto: Chris Emil Janssen/dpa/picture alliance

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi sharhinta ne kan maido hulda mai karfi tsakanin kasashen Masar da Turkiya. Jaridar ta ce, abokan gaba sun ziyarci juna. Bayan kawo karshen sabanin da ya faru tsakaninsu shugaban kasar Masar ya kawo ziyara wa takwaransa na Turkiya Raccep Tayyip Erdowan. Domin nua irin girmamawa da yake yi wa bakon shugaba Erdowan da kansa ya je har tashar jiragen sama ya tarbi Abd al-Fattah al-Sisi na kasar Masar, mutumin da har a 'yan shekarunnan Erdowan ke kiransa wanda ya yi juyin mulki kuma shugaban kama karya. A yanzu kasar da ke arewacin Afirka ta kasance babbar kawa kuma ana ganin kasashen biyu suna cikin mafiya karfin fada aji a rikicin Gabas ta Tsakiya.

Hoto: Murad Sezer/REUTERS

Jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi nan ba da jimawa ba Jamus za ta rika samun makamashi marar gurbata mahalli daga kasar Namibiya. Inda jaridar ta ruwaito ministan tattalin arzikin Jamus Robert Habeck na mai cewa kasar Namibiya tana da kyakkyawar damar samar da makamashi wadatacce kuma marar gutbata mahalli. Jamus dai tana ta bin duk inda ta samu kofa don samarwa masana'antunta makamashi, a dai dai lokacin da kasashen Turai suke neman maye gurbin kasar Rasha a batun samun makamashi. Amma masu kare mahalli suka ce ba komai ba ne illa abun kunya ga kasar Jamus bayan abin da ta aikata lokacin mulkin mallaka da ta yi wa Namibiya.

Hoto: Str/Xinhua/picture alliance

Za mu waiwayi ga jaridar die Tageszeitung waccce ta ce boren fursononi da ke daure a gidajen yari da kuma babbar rudani a Kinshasa babban birnin JDK. Inda a cikin rudanin aka yi kiyasin mutane 129 suka mutu wasu da dama suka jikkata a tarzumar gidan yarin. Rahotanni suka ce mummunan yanayin da Fursunonin ke ciki shi ne ya sa suka fusata abin da ya kawo rudu a gidan yarin Makala wanda shi ne mafi girma a fadin kasar.