Jaridun Jamus : 07.08.2026
August 7, 2026
Der Tagesspiegel ta nemi sanin " Dalilin da ya sa mutane da yawa ke son barin Maroko, kasar da ta fi kowacce saurin bunkasa a yankin arewacin Afirka." A lokacin da take ba da amsa a cikin sharhinta, jaridar ta ce ginin layin dogo na jiragen kasa masu gudu da gina filayen wasa don daukar nauyin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da Maroko ke yi na burge duniya. Amma su 'yan asalin Maroko musamman ma matasa na son ayyukan yi da asibitoci masu inganci da suka rasa, lamarin da ke sa su yunkurin kaura zuwa Turai.
Ita kuwa Neue Zürcher Zeitung ta ce Maroko na daukar Iyakar a matsayin makami, saboda ana zargin gwamnatin Maroko da barin kwararar bakin haure da gangan. Amma a shrhinta mi taken " laifi tudu ne, kullum yana kan wani", Berliner Zeitung ta ce bayan kwararar bakin haure zuwa Ceuta, Sifaniya da Maroko sun yi fama wajen shawo kan lamarin. Sai dai dalilai marasa tushe kan musabbabin kwarar bakin hauren na karade kafofin sada zumunta.
A game da kalubalen tsaro da kasashen Afirka ke fama da shi kuwa, Die Tageszeitung da ake wallafawa a kullum ta ce " na ci gaba da samun gindin zama a Kenya." Jaridar ta ce kungiyar Al-Shabaab da ke gagwarmaya da makamai a Somaliya na fadada barazanarta ga daukacin yankin gabashin Afirka baki ɗaya. Wannan ba ya rasa nasaba da hada kai wajen yin aiki da kungiyar 'yan tawayen Houthi da Iran ke marawa baya a Yemen.
Die tageszeitung ta ce kungiyar Al-Shabaab ta sake yin kwanton bauna ga 'yan sandan Kenya da aka horar don yaki da ta'addanci, inda ta halaka biyar daga cikinsu. Wannan ba shi ne hari na farko da 'yan bindigan Somaliya ke kai wa Kenya a cikin 'yan makonnin nan ba. Ko a watan Yulin da ya gabata, dakarun Kenya sun gano wani sansanin 'yan Al-Shabaab a gundumar Mandera. Jaridar ta ce tun fiye da shekaru 20, 'yan ta'adda Al-Shabaab ke barna a Somaliya tare da rubanya kai hare a Kenya a baya-bayan nan.
Idan muka koma kan batun tattalin arzikin kuwa, Welt plus ta yi sharhi ne kan abin da ta danganta da "hauhawar farashin koko da romon bai ta taba kaiwa ga manoma ba." Jaridar ta ce a shekaru biyu da suka wuce, farashin koko ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin duniya. Amma manoman da ke kasashen Afirka kamar Côte d' Ivoire da Ghana ba su amfana da komai ba, kuma ga shi a yanzu sun sake komawa gidan jiya a fannin faduwar farashin hajarsu.
A lokacin da ta ruwaito labarin Bony Alain Dechi, da ke noma koko a Agboville da ke Côte d' Ivoire, Weltplus ta ce faduwar farashi ya dakushe mafarkinsa na shekaru biyu da suka wuce, na gyaran gidan tare da mallakar mota. A maimakon haka, jaridar ta ce ya shiga cikin halin tasku saboda farashin koko ya sake yin kasa sosai, alhali a shekarar 2024, farashinsa ya kai matsayi mafi girma a tarihi, inda ake sayar da tan daya a kan sama da dala 12,000; ma'ana ya ninka sau akalla hudu.
Za mu karkare da fannin kiwon lafiya, inda a lokacin da ta ci gaba da bibiyar inda aka kwana game da yakin da cutar Ebola a Kwango, Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce cutar "na ci gaba da yaduwa." Jaridar ta ce yanzu haka an yi rejistar wadanda suka kamu da Ebola a larduna biyar a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, wadanda suka hada da Ituri, arewacin Kivu, kudancin Kivu, Haut-Uélé, da Tshopo. Sai dai hukumar lafiya ta duniya WHO na gwajin wata allurar rigakafin wannan annoba mafi girma da aka taba samu a kasar Kwango.
Frankfurter Allgemeine Zeitung ta kara da cewa, an fara wani bincike kan maganin Ebola a yankin da cutar ta bulla, kuma wani mai neman allurar rigakafi yana gwajin mataki na farko. Jaridar ta ce ba a san ko allurar rigakafin VSV-Ebov da masana kimiyyar Jamus suka taimaka wajen samarwa a 2019 kan cutar Ebola da ake kira Zaire, tana ba da kariya ga nau'in Bundibugyo ba.