1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus : 14.11.2025

November 14, 2025

Yakin da ake gwabzawa a Sudan da rikicin siyasa a Zambiya da sakin da hukumomi suka yi wa, wani marubuci a Aljeriya sune batutuwan da Jaridun Jamus suka ambato,

Shugaban Zambiya Hakainde Hichilema
Shugaban Zambiya Hakainde Hichilema Hoto: Peng Lijun/Xinhua/picture alliance

Ba a abin da ya fi daukar hankalin jaridun Jamus kan Afirka a wannan mako fiye da rikicin da ke ta'azzara a Sudan da ke zama kasa ta uku mafi girma a nahiyar. A lokacin da take tsokaci, jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce rundunar RSF ta fara amincewa da shirin tsagaita wuta, kafin daga bisani ta lashe amanta ta hanyar kai hare-hare da jiragen sama marasa matuki a Omdurman da Atbara. Ita kuwa rundunar sojin kasar ta ce babu gudu babu ja da baya matukar abokan gaba ba su ajiye makamai ba, matakin da jaridar ta ce da kamar wuya ya afku.

Dakarun RSFHoto: Mohamed Babiker/Photoshot/picture alliance

Ita kuwa Frankfurter Allgemeine Zeitung a karkashin sharhinta mai taken: "Mafaka ta karshe a Arewacin Darfur", ta ce a yankin da ke fama da yaki a kasar Sudan, mutane na ba da rahoton yunwa da gudun hijira da kuma matsalolin kiwon lafiya da suke fama da su. A nata bangaren, Zeit Online ta ruwaito cewar ministan harkokin wajen Jamus Johann Wadephul ya yi kira da a tsagaita wuta a Sudan. Jaridar ta ce  takwarorinsa ma na Australiya da Island da Canada da Nowey a Burtaniya da kasashen EU guda 10, sun yi tir da abin da suka kira kisan gillar da ake yi wa jama'a a Sudan, lamarin da suka danganta da keta dokokin kasa da kasa.

Batu na biyu da ya fi shiga kanun labaran Jamus shi ne sakin marubuci Boualem Sansal da shugaban kasar Aljeriya ya yi bisa taimakon kasar Jamus. Süddeutsche Zeitung ta ce Boualem Sansal ya samu 'yanci bayan ya shafe shekara guda a tsare a Aljeriya, inda shugaban kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya amince da bukatar afufwa da takwaransa na Jamus Frank-Walter Steinmeier ya mika masa. Jaridar ta ce Sansal ya sauka a Berlin domin samun kulawar lafiya, amma watakila zai iya tafiya zuwa Faransa nan ba da jimawa ba.

Sojojin gwamnatin SudanHoto: Sudanesische Streitkräfte/AP/dpa/picture alliance

Ita kuwa die Tageszeitung ta yi sharhi mai taken: "Godiya, Berlin" bayan da aka yafe wa Sansal laifin sukar gwamnati da ya aikata. Jaridar ta ce, Steinmeier ya cimma abin da shugaban Faransa Emmanuel Macron da ministocinsa da masu wallafa littatafai ba su iya cimmawa ba.

Ita kuwa die Tageszeitung ta tabo siyasar Zambiya, inda ta fara ta tambaya ko Hakainde Hichilema ne zai zama shugaba na gaba da zai fuskanci fishin matasa na Gen Z ? Jaridar da ake buga wa a kullum ta ce daruruwan mutane sun mutu a zanga-zangar kin jinin gwamnati da matasa suka shirya a zaben shugaban kasar Tanzaniya. Amma bai hana Hakainde Hichilema zama daya daga cikin shugabannin Afirka hudu da suka halarci bikin rantsar da Samia Suluhu Hassan ne.

Boualem Sansal marubbucin kasar Aljeriya da aka sakoHoto: Nicolas Roses/ABACA/picture alliance

Die tageszeitung ta kara da cewar, kasancewar Hakainde Hichilema na da niyyar sake tsayawa takara a zaben watan Agusta na 2026, zanga-zangar Gen Z na iya isa kasarsa ta Zambiya. A wani abin da ke zama somin tabi, jaridar ta ce rikici ya barke a gundumar Chingola da ke yankin hakar ma'adinai na arewacin Zambiya yayin da Shugaba Hichilema ya kai ziyara. Matasa da yawa da aka tsara za su yi magana sun buge da fasa shaguna, kuma suka yi ta bi ayarin motocinsa da harbi,  lamarin da ya sa aka kwantar da Shugaba Hichilema a asibiti sakamakon rauni a kai.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani