1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jaridun Jamus :15.05.2026

Zainab Mohammed Abubakar AH
May 15, 2026

Taron kasashen Afirka da Faransa a Kenya da rikicin siyasar Afirka ta Kudu da kuma batun taimakon Jamus a Sudan sune suka dauki hankali a Jaridun Jamus.

Taron Faransa da Afirka 2026
Taron Faransa da Afirka 2026Hoto: Luis Tato/AFP

 Jaridar die Tageszeitung ta wallafa sharhi mai taken "Jamus ta yi alkawarin bayar da agajin jin kai mai yawa ga wadanda yakin Sudan ya shafa. Amma da alama bai kai yawan  abin da aka sanar ba"

Jaridar ta ce, a taron kasa da kasa na Sudan da ta shirya a Berlin a ranar 15 ga watan Afrilu, gwamnatin Jamus ta yi alkawarin bayar da tallafin jin kai na Yuro miliyan 232 ga Sudan, miliyan 212 daga kasafin kudin ofishin kula da harkokin waje da kuma wani miliyan 20 daga kasafin kudin ma'aikatar tattalin arziki da ci gaban tarayya (BMZ). Amma kadan ne kawai daga cikin wannan adadin zai isa ga mabukata na Sudan a wannan shekarar.

Wannan ya bayyana ne daga martanin gwamnatin Jamus ga binciken majalisar dokokin kasar. A cewar martanin, an ware Yuro miliyan 37.5 kacal a matsayin kudaden da Sudan din za ta samu a wannan shekarar ta 2026. Kuma a bayyane yake, an riga an raba mafi yawan wannan kudin, a wasu lokuta ma kafin taron n Berlin.

Hukumar bin diddigin kudi ta ofishin MDD kan harkokin jin kai (OCHA) don taimakon Sudan, ta ba da rahoton cewa kudaden da Jamus ta bayar a wannan shekarar sun kai dalar Amurka 26, kasa da Yuro miliyan 22 kenan. Gwamnatin Jamus ta ayyana wannan adadi a matsayin kusan Yuro miliyan 26, kuma ta tabbatar da cewa kudin wani bangare ne na alkawarin tallafin da aka yi a taron Sudan.

"Ziyarar 'yan'uwa" wanna shi ne taken sharhin da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta wallafa inda ta ce

Emmanuel Macron yana kokarin wanke sunan Faransa a Afirka a wani taro da aka yi a Nairobin Kenya.

'Yan kasar SudanHoto: WDR

Cikin kasa da minti guda shugaban Faransar da takwaransa na Kenya da kuma na Senegal suka buga wasan kwallon kafa a ranar Litinin cikin raha da tafi na 'yan kallo wanda shi ne mabudin babban taron na Afirka da Faransa.

Wannan shi ne ainihin hoton da Macron yake son nuna wa Afirka a kwanakin nan, cewar Faransa tana mataki daidai da ita, ba wai tana gaba da Afirka ba. Hasali ma za su yi aikin hadin gwiwa, kamar yadda ya nuna a wurin filin kwallon kafa na a jami'ar Nairobi, a gefen babban taron Faransa da Afirka wanda ya gudana a ranaikun Litinin da Talata a babban birnin Kenyar.

Shugabanni sama da 30 ne suka yi tattaki zuwa Nairabo daga dukkan sassan nahiyar Afirka, daura ga Macron, wanda ya taka rawa a matsayin mai masaukin baki tare da shugaban Kenya William Ruto. Taron mai cike da tarihi ya tattauna batutuwan da suka hada da saka hannun jari da masana'antu da zaman lafiya da tsaro da kuma sauyin yanayi. Sai kuma kuma uwa uba matsayin Faransa a Afirka.

Taron Faransa da Afirka a Kenya 2026Hoto: Thomas Mukoya/REUTERS

Bari mu karkare sharhunan jaridun na Jamus da labarin da jaridar Berliner Zeitung me taken "Shugaba Cyril Ramaphosa ya ki yin murabus duk da tsare tsaren tsige shi.

Jam'iyyarsa ta ANC yanzu haka tana fuskantar matsin lamba. A wani jawabi da ya yi wa al'ummar kasar a talabijin a ranar Litinin da maraice, ya yi kokarin kawo karshen sabuwar badakalar da ta dabaibaye shi, wanda ya zama umul aba'isin tayar da sabbin tsare-tsaren tsige shi da majalisar dokoki ta yi. Ya jaddada muhimmancin zaman lafiya kwanciyar hankali da ci gaba, da kuma girmama tsarin kundin tsarin mulki. In da ya ce gwamnatinsa na ci gaba da mai da hankali kan farfado da tattalin arziki da samar da ayyukan yi musamman tsakanin matasa.

Cyril RamaphosaHoto: Willy Kurniawan/REUTERS

Ramaphosa na fuskantar matsin lamba tun bayan wani hukunci mai cike da cece-ku-ce da kotun tsarin mulki ta yanke a ranar Juma'a da ta gabata. Babbar kotun Afirka ta Kudu ta yanke hukuncin cewa dole ne majalisar dokokin Afirka ta Kudu ta sake yin la'akari da tsige shugaban. 'Yan majalisar ANC masu rinjaye a majalisar sun hana daukar irin wannan mataki a shekarar 2022, amma yanzu 'yan adawa sun yi nasara, kasancewar alkalan sun yanke hukuncin cewar matakin ya saba wa kundin tsarin mulki.))

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani