Jaridun Jamus : 17.04.2026
April 17, 2026
Jaridar die Tageszeitung ta mayar da hankali kan ziyarar aikin kwanaki 10 da shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika na duniya, Fafaroma Leo na 14 ya fara a kasashen Aljeria, Kamaru, Angola, da Equatorial Guinea, ziyarar da take da tasiri a wannan nahiya ta Afirka da ake kara samun bunkasan mabiya addinin Kirista.
Fafaroma Leo na 14 ya fara wannan ziyara daga kasar Aljeriya da ke yankin arewacin Afirka, wadda take da jama'a gabili mabiya addinin Islama, abin da ke nuna matakin neman ganin hadin tsakanin mabiya addinan biyu. Mai magana da yawun fadar Vatikan, Matteo Bruni, ya tabbatar da wannan batu na neman hadin kai ganin cewa kaso 99 cikin 100 na mutanen Aljeriya kimanin milyan 47 sun kasance mabiya addinin Islama.
Ita kuma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta mayar da hankali kan cika shekaru uku da fara yakin basasa na kasar Sudan, inda ranar 15 ga wannan wata na Afrilu da aka cika shekaru uku da fara yakin aka gudanar ta taron neman sake gina kasar ta Sudan a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus. Yayin da ake batun tara kudin na taimakon kasar ta Sudan, babu wata mafita da aka samu na kawo karshen wannan yaki. Lokacin taron an yi alkarin samar da kudi kimanin Euro Bilyan 1.3 (Euro milyan dubu da dari uku), daga ciki Jamus za ta bayar da kimanin Euro milyan 230 na taimakon jinkai.
Sai kuma jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta yi sharhin mai take Jamhuriyar Benin ta samu sabon shugaban kasa. Jaridar ta ce 'yan watanni bayan yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin da ke yankin yammacin Afirka, yanzu kasar ta yi sabon shugaban kasar da aka zaba, Romuald Wadagni mai shekaru 49 da haihuwa kana ministan kudi, wanda ya smau goyon bayan Shugaba Patrice Talon.
Shi dai Shugaba Talon kundin tsarin mulkin ya hana masa takara bayan kammala wa'adin mulki na biyu. Ita dai Jamhuriyar Benin ta kasance karamar kasa mai mutane kimanin milyan 15, wadda take makwabtaka da Najeriya. Jamhuriyar Benin karkashin Shugaba Talon ta smaun bunkasa tattalin arziki amma ta fuskanci matsaloli takurawa 'yan adawa na siyasa.
Ita kuwa jaridar Welt online ta ce kasar Faransa ta janye gayyatar da aka bai wa kasra Afirka ta Kudu a taron kungiyar G7 na gaggan kasashe masu arzikin masana'antu na duniya na gaba, da ake ganin matakin na da dangantaka kan matsin lamba daga gwamnatin Amirka, wadda ba ta dasawa da Afirka ta Kudu. Masana na ganin haka a matsayin zagon kasa ga muradun kasashen Yammacin Duniya da ke neman samun tasiri a nahiyar Afirka, inda kasar China take kara samun tagomashi.
Wani na hannun daman Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya karya batun na janye gayyatar Afirka ta Kudu zuwa taron na G7 na watan Yuni sakamakon matsin lamba daga Amurka, inda ya ce a gaba daya aka amincewa cewa kasar Kenya ta wakilci nahiyar Afirka a wajen taron.