1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jaridun Jamus : 17.10.2025

Abdullahi Tanko Bala AH
October 17, 2025

Batun rasuwar jagoran adawa na Kenya Raila Odinga da zaben Kamaru da kuma rikicin siyasar Tanzaniya sun dauki hankali a Jaridun Jamus.

Hoton tsohon firaminstan Kenya  Raila Odinga
Hoton tsohon firaminstan Kenya Raila OdingaHoto: Monicah Mwangi/REUTERS

Jaridar die tageszeitung a sharhinta mai taken dan gwagwarmayar neman sauyi na Kenya Raila Odinga ya rasu a wani asibiti a kasar Indiya. Jaridar ta ce Kenya na cikin jimami, daya daga cikin manyan 'yan siyasar kasar ya rasu a wani asibitin ido a Indiya a sakamakon bugun zuciya.

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya ayyana zaman makoki na kwanaki bakwai ita ma majalisar dokoki ta tafi hutu domin jimamin dan siyasar. Jama'a sun yi dafifi a gidan Odinga da titunan kasar dauke da ganyen kwakwa da ke nuna alamar an shiga makoki.

Mutuwar Raila Odinga ta taba kowa a Kenya. Ya sauya salon siyasar kasar a farkon shekarun 1990 inda aka kawo karshen tsarin mulki na Jam'iyya guda daya tilo. Mahaifinsa Oginga Odinga ya taimaka wajen jagorantar Kenya ga samun 'yancin kai daga Burtaniya a 1963.

Raila Odinga ya tsaya takarar neman shugancin Kenya har sau biyar amma bai samu nasara ba. Duk da rashin nasararsa a zabbuka ya kasance dan siyasa mai matukar tasiri. Raila wanda aka haife shi a shekarar 1945 ya zauna a tsohuwar tarayyar Jamus inda ya yi karatu tsakanin shekarun 1962 zuwa 1990 a Leipzig da kum Magdeburg. Mutum ne mai ra'ayin gurguzu akidar da ya rike duk tsawon rayuwarsa. Shugaban Kenya William Ruto a sakon sa na ta'aziyya ya baiyana Odinga da cewa mutum ne wanda ba ya shayi wajen fada wa mahukunta gaskiya komai dacinta.

Gawar Raila Odinga tsohon firaministan KenyaHoto: Andrew Kasuku/AP Photo/picture alliance

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi nata sharhin a kan shirin zaman lafiya a Gaza inda ta ce Masar na son yin amfani da shirin zaman lafiyar na Gaza domin samun damar taka rawa a kasashen Larabawa.

Jaridar ta ce Gaza na da muhimmanci a tsarin Gabas ta Tsakiya. Sakamakon tsagaita wuta da aka cimma da Israila da kuma Masar wadda ta tsaya a madadin Hamas sannan da taron koli da aka gudanar kan sulhun a Sharm el Sheikh, nan da nan Masar ta dawo tsakiyar yunkurin diflomasiyya a matsayin mai shiga tsakani da kuma tasiri a yankin.

Shugaba Abdelfatah al Sisi wanda tsawon lokaci manufofinsa na harkokin waje yake kai komo tsakanin nuna dattako da taka tsan-tsan kan tsaro da shugabanci a yankin yana kallon kansa a matsayin wanda zai ba da gudunmawa saboda Masar ba kawai za ta iya shiga tsakani ba ne kadai wajen yin sulhu tana iya bayar da kariya ta tsaro da samar da daidaito na tsaka-tsaki duk da a waje guda tana fuskantar matsin lamba a cikin gida. Saboda haka matsin lambar da ke kan shugaba al Sisi shi ne yadda a cikin gida zai yi kokarin cika muradun al'umma tsakanin wadanda ke goyon Falasdinawa da masu goyon bayyan Isra'ila a manufofinsa na harkokin waje ba tare da ya tsoma kansa cikin rikici ko yaki ba.

Abdel Fattah el-Sisi Shugaban Kasar MasarHoto: JAVIER SORIANO/AFP/Getty Images

Jiran tsammani cikin shauki a Kamaru shi ne taken sharhin Jaridar Jaridar Süddeutsche Zeitung.

Jaridar ta ce tashin hankalin da ya faru a garin su jagoran dan takarar adawa Issa Tchiroma Bakary yana neman mamaye batun sake zaben shugaba Paul Biya. Tuni dai kawancen jam'iyyun hadaka da suka mara wa Tchiroma suka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.

A ranar Lahadin da ta gabata ce (12.10.2025) 'yan Kamaru suka kada kuri'a a zaben da ake sa ido Paul Biya mai shekaru 92 a duniya ke neman tazarce. Shugaban wanda shi ne ya fi tsufa a cikin shugabannin kaashen duniya ya shafe shekaru 43 yana mulki.

Zaben Kamaru ana kidayar kuri'uHoto: Wang Ze/IMAGO

Zabe a Kamaru dai shekaru da dama an dade ana zargin magudi da zamba. Hukumar zabe ta Elecam na shan suka kan rashin gaskiya da fayyace komai a faifai. Sakamakon zaben ba zai samu ba kafin ranar 26 ga watan Oktoba.

A nata bangaren Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi sharhi ne a kan jagoran adawa a Tanzaniya Tundu Lissu wanda ake zargi da cin amanar kasa. Jam'iyyarsa ta yi korafin cewa bita da kulli ne ake yi masa.  

Jagoran adwa na Tanmzaniya Tundu Lissu Hoto: Emmanuel Herman/REUTERS

Tundu Lissu, shugaban Jam'iyyar Chadema babbar Jam'iyyar adawa a Tanzaniya an kama shi ne a watan da ya gabata kan zargin wasu kalamai inda ya yi kira ga 'yan Tanzaniya su bijire wa zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da aka shirya gudanarwa a ranar 29 ga wannan watan na Oktoba.