1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jaridun Jamus: 19.07.2024

Usman Shehu Usman AH
July 19, 2024

Jaridun na Jamus sun ambato batun yakin Sudan da zanga-zagar Kenya da kuma zaben Ruwanda.

Hoto: Wang Hao/Xinhua/IMAGO

A yau jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung za ta bude mana sharhunan Jaridun na Jamus kan nahiyar Afirka, inda jarida ta duba mummunan yaki da ke faruwa a Sudan. Jaridar ta ce rikici a Sudan ya kara tsananta kusan 'yan gudun hijirar da yaki ya kora sun kai miliyan 10.6. Kai Jaridar ta ce wannan fa shi ne rikicin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya a halin yanzu kuma yana ci gaba da ta'azzara. Hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya wato (IOM) ta sanar da adadin a cikin sabon rahotonta, wanda aka wallafa a wannan mako. Kusan kashi uku cikin hudu sun gudu ko kuma sun rasa matsugunansu tun bayan barkewar yakin baya-bayan nan a watan Afrilun 2023, wato kashi biyar na al'ummar kasar. Sama da mutane miliyan 2.2 ne suka tsere zuwa wasu kasashe, sauran kuma suna cikin iyakokin Sudan. Hakan na nufin daya daga cikin bakwai da ke gudun hijira a duniya ya fito ne daga kasar ta Sudan da ke gabashin Afirka.

Hoto: Monicah Mwangi/REUTERS


Sai kuma kasar Kenya da ita ke a gabashin Afirka. Inda jaridar Der Tagesspiegel ta ce zanga-zangar jama'a kuma karkashin jagorancin matasa za ta iya hambarar da shugaban kasa? Jaridar ta ci gaba da cewa a ranar Alhamis din makon jiya ne shugaban kasar Kenya William Ruto ya fitar da sanarwar a cikin sanar an kori dukkan ministoci da babban mai shari'a daga mukamansu ba tare da bata lokaci ba. Sai dai kawai firaminista, wanda kuma ke jagorantar ma'aikatar harkokin waje. A cikin sanarwar Ruto ya sanar da cewa daga yanzu zai ci gaba da tattaunawa tare da 'yan kasar don dora gwamnati a kan turba gaba, amma kuma bisa dukkan alamu masu zanga-zangar ba su kai ga hakura ba.

Hoto: Brian Inganga/AP Photo/picture alliance

Ita kuwa jaridar die tageszeitung sharhinta kan zaben kasar Ruwanda ne, inda ta ce a bisa dukkan alamu kashi 99 cikin 100 ne ke goyon bayan shugaba Paul Kagame na Rwanda, wanda ya hau kan karagar mulki tun a shekarun 1990. Yanzu an sake ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe. Sakamakon ba abin mamaki ba ne, inda kashi 99.15 na kuri'un da aka kada, shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya sake lashe zaben a karamar kasar da ke gabashin Afirka. Sama da ofisoshin zabe 2,500 ne aka rufe da misalin karfe uku na yammacin ranar Litinin, sannan aka fara kidayar kuri’u. Da yammacin ranar ne hukumar zaben kasar ta sanar da sakamakon wucin gadi bayan da ta kirga kusan kashi 80 cikin 100 na katunan zabe.