Jaridun Jamus: 26.09.2025
September 26, 2025
Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung da ta mayar da hankali kan sakamakon zaben Malawi, ta danganta nasarar komawa kan karagar mulki da Peter Mutharika mai Shekara 85 ya yi da " Kome irin na Demokaradiyyaa". Jaridar ta yaba matakin da shugaba mai barin gado Lazarus Chakwera na jam'iyyar MCP ya dauka, na amince da shan kaye tare da taya abokin hamayyarsa Mutharika barka da arziki, tun kafin hukumar zaben kasar da ke kudu maso gabashin Afirka ta bayyana sakamakon a hukumance .
Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce mika mulki cikin ruwa sanyi ya kawar da fargabar tashin hankali da ake da ita, bayan da manyan 'yan takaran biyu suka sha alwashin lashe zaben Malawi.
Sai dai dawowar tsohon shugaban kasa Peter Mutharika kan mulki ba ya nufin amincewa da manufofinsa 100%. Hasali ma, da yawa na sukar kamun ludayinsa a wa'adinsa na farko daga 2014 zuwa 2020. Amma mummunan halin talauci da koma bayan arziki da Malawi ke ciki a mulkin Lazarus Chakwera ya sa al'umma tunawa da bara saboda ba su ji dadin bana ba.
Ita kuwa die Tageszeitung ta yi sharhi mai taken "Masu juyin mulkin na yankin Sahel sun juya wa kotun duniya baya", bayan da kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso suka sanar da janyewa daga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta ICC. Jaridar ta ce a bisa ka'ida, wannan mataki ba zai iya fara aiki nan take, sai dai bayan shekara guda. Sannan, kotun ta duniya na da hurumin shari'a kan abubuwan da suka faru kafin janyewar.
Sai dai a aikace, akwai yiyuwar kawo karshen hadin gwiwar da ke tsakanin The Hague da Bamako da Ouagadougou da Niamey, yayin da rahotanni daga kasashen AES ke ci gaba da nuna cin zarafin da sojoji da kawayensu na Rasha ke yi wa fararen hula.
A hirar da die Tageszeitung ta yi da shi, wani manazarci dan kasar Mali mai suna Séga Diarrah, ya nuna fargaba kan karuwar hadarin rashin hukunta masu aikata manyan laifuka da kungiyoyin masu dauke da makamai da kuma sojojin gwamnati suke aikata ba daidai ba. Saboda haka ne jaridar ke ganin cewar "fararen hula da abin ya shafa sun rasa wata hanyar kasa da kasa da za su iya jin muryarsu."
Yanzu kuma sai mu je ga jaridar Zeit Online da ta yi tsakaci kan matakin da shugaban Kasar Masar al-Sissi ya dauka na yafe wa fitaccen dan gwagwarmaya Alaa Abdel Fatah da wasu fursunoni biyar laifin da aka same su da aikatawa. Jaridar ta yi waiwaye kan fafutukar da Abdel Fatah ya yi, inda ta danganta mawallafin, kuma mai rubutu ra'ayinsa ta yanar gizo, da daya daga cikin manyan jagororin Juyin juya halin 2011 da ya kawar da Hosni Mubarak daga mulki.
Kamun karshe da aka yi wa Alaa Abdel Fattah ya gudana ne a 2019, inda aka yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar a 2021 saboda yada labaran karya. ZEIT ONLINE ta kara da cewa, masu rajin kare hakkin bil adama na zargin Masar da murkushe masu sukar gwamnati, wacce ta hana gudanar da zanga-zanga. Sannan akwai rahotannin azabtarwa da sauran nau'ikan zalunci a gidan yari. Dadin dadawa ma dai, kungiyoyin kare hakkin bil adam suka ce akwai fursunonin siyasa 60,000 a Masar.
A karshe die Tageszeitung da ta yi sharhinta kan matakin shari'a da 'yan Afirka ta yamma 11 suka dauka bayan da gwamnatin Ghana ta tsare su tun lokacin da aka tasa keyarsu daga Amurka. Jaridar ta ce a farkon watan Satumba ne, aka koro jimillar 'yan Afirka ta Yamma 14 daga Amurka zuwa Ghana, amma ba tare da dan asalin kasar ko daya ba. Sannan ta kara da cewar ko yake uku sun koma kasashensu, amma 11 na tsare a sansanin sojoji na Bundase mai tazarar kilomita 70 da Accra ba tare da gurfanar da su a gaban wata kotun Ghana ba, lamarin da ya saba wa doka.
Die Tageszeitung ta ce rayuwar wasu daga cikin wadanda aka koro za ta kasance cikin hadari idan aka tasa keyarsu zuwa kasashensu na asali. Saboda haka ne lauyansu Oliver Barker-Vormawor ya shigar da kara. Kuma bayanai na cewa, hudu daga cikin su 'yan Najeriya ne, uku daga Togo, biyu daga Mali, daya daga Gambia da daya daga Laberiya.