1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Ceto 'yar Chibok ya karfafa guiwa

Mohammad Nasiru AwalMay 20, 2016

Ceto daya daga cikin 'yan matan makarantar sakandaren garin Chibok da ke a jihar Bornon Najeriya ya dauki hankalin jaridun Jamus.

Nigeria Präsident Buhari empfängt befreites Schulmädchen Amina Ali
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

A labarinta mai taken an ceto 'yar makarantar Chibok daga cikin wadanda Boko Haram ta yi garkuwa da su, jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce bayan sama da shekaru biyu, daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa ta kubuta daga hannun 'yan tsagerun masu tsattsauran ra'ayin addini. A wasu makonnin da suka wuce wata da ta yi kama da 'yar kunar bakin wake da ta mika kanta ga mahukuntan kasar Kamaru ta yi ikirarin cewa ita 'yar garin Chibok ce, amma daga baya aka gane cewa karya ta yi. Sai dai a wannan karon wadda aka ceton mai suna Amina Ali hakika 'yar Chibok ce, kuma an rawaito tana cewa dukkan 'yan matan na Chibok, Boko Haram na tsare da su a dajin Sambisa, amma shida daga cikinsu sun rasu.

Ta'addanci ya ruguza harka a gabar teku

Gabar teku ta kasance wayam tun bayan harin ta'addancin da kungiyar al-Qaida ta kai, inji jaridar Die Tagezeitung, inda ta kara da cewa.

Arouna Ouattara wani ma'aikacin gidan abinci a Grand BassamHoto: DW/J.-P. Scholz

Tun bayan harin da ya hallaka mutane 22 da kungiyar al-Qaida reshen arewacin Afirka ta kai a yankin shakatawar nan na Grand Bassam da ke a bakin tekun kasar Cote d'Ivoire, har yanzu wannan wuri bai farfado ba. Wani mai mashaya a yankin ya ce tun bayan harin na ranar 13 ga watan Maris, 'yan yawon shakatawa sun kaurace wa yankin da tun a shekarar 2012 kungiyar ilimi, kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta sanya shi a jerin wurare masu dinbim kayayyakin tarihi na duniya, saboda dinbim tsofaffin gidaje da aka sake yi wa kwaskwarima.

Bisa ga alamu CIA ta yi wa Mandela leken asiri

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung a wannan makon ta leka kasar Afirka ta Kudu ne tana mai cewa bisa ga dukkan alamu hukumar leken asirin Amirka ta CIA ta taba yi wa tsohon shugaban Afirka ta Kudu marigayi Nelson Mandela leken asiri.

Daga hagu Cyril Ramaphosa, Nelson Mandela da Jacob Zuma a wani taron ANC a Johannesburg a 20.12.1991Hoto: Getty Images/AFP/W. Dhladhla

Ta ce sabbin bayanai sun nuna irin rawar da CIA din ke takawa a kasar ta Afirka ta Kudu. Jaridar ta rawaito wani tsohon jami'in diplomasiyyar Amirka kuma dan CIA Donald Rickard da ya taba aiki a Afirka ta Kudu wanda a cikin wata hira da wani mai shirya fim dan Birtaniya, John Irvin, ya ce bisa umarnin CIA ya ba wa gwamnatin wariyar launin fatar Afirka ta Kudu bayanai da suka kai ga cafke Nelson Mandela a shekarar 1962. Dan CIA dai bai nuna nadama ba, domin a cewarsa a lokacin Mandela ya kasance wani dan kwaminis mafi barazana bayan Tarayyar Sobiet. Shi dai tsohon dan gwagwarmayar na kungiyar ANC ya kwashe fiye da shekaru 27 a gidan maza, amma a karshe ya zama shugaban Afirka ta Kudu bakar fata na farko.