Sharhunan Jaridun Jamus kan AFCON da Sudan
December 26, 2025
Jaridar Sportbild ta yi sharhi a kan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, mai taken "Duk abin da kuke bukatar sani game da Najeriya: Super Eagles na son sake hawa sama"! Lokacin da aka fara gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afirka a Maroko cikin watan Disambar shekara ta 2025 da ke ban kwana, Najeriya ta kasance cikin manyan kasashen da ake so.
Guda daga cikin kungiyoyin kwallon kafa mafi nasara a Afirka tsawon shekaru masu yawa, lamarin da ya ba ta damar kafa tarihi mai kyau a fannin wasannin, a cewar jaridar da ke sharhi kan wasannin motsa jiki ta Sport bild. Najeriya ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka AFCON har sau uku: Na farko a 1980 sai a 1994, da kuma 2013.
Kazalika ta kuma lashe lambar zinare ta wasannin Olympics a Atlantan Amurka, a shekarar 1996. Kungiyar ta kai zagaye na 16 sau uku a gasar cin kofin duniya, shekarar 1994 da 1998 da kuma 2014. A gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar ta Afirka da ta gabata a 2023/2024, Najeriya ta kai wasan karshe sai dai ta sha kashi a hannun mai masaukin baki Côte d'Ivoire.
Da wannan gogewa kana da Éric Chelle mai shekaru 47 a matsayin sabon mai horarwarsu, Super Eagles na da kwarin gwiwa sosai a gasar ta bana. Tuni ta buge takwarorinta na Tanzaniya ,a wasan farko a ranar Talata da ci biyu da daya. Manufarsu a wannan gasa ita ce, lashe kofin a karo na hudu da kuma sake darewa sama a fannin kwallon kafar nahiyar.
"Waraka a yayin gudun hijira" wannan shi ne, taken labarin da jaridar die tageszeitung ta wallafa a kan halin da likitocin da suka yi gudun hijira daga Sudan ke ciki a ketare. Jaridar ta ce, likitocin Sudan sun tafka yaki da gwamnatin mulkin soja. Yakin da ya tilasta musu guduwa zuwa ketare, inda a yanzu wasu daga cikinsu suka gina sabon asibiti a Kampala babban birnin kasar Yuganda domin taimakon 'yan kasarsu da ke samun mafaka a sansanoni dabam-dabam.
Likitan hakori Shimaa Mahmoud cike da murmushi na kunna karatun alkur'ani a mai sanyaya zuciya a kwamfutarta, a wasu lokuta kuma sautin kidan Sudan ne mai tausasa zuciya cikin harshen Larabci. A cewarta: "Majinyata suna jin tsoron ciwon hakori, don haka na kan sanya irin wadannan sautukan domin kwantar da hankalinsu kadan." Likitar hakorin mai shekaru 29 na zaman daya daga daruruwan likitocin Sudan da suka tserewa yakin kasarsu, kuma ke bayar da tallafi ga 'yan uwansu da ke gudun hijira a sassan da suke.
Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, cewa ta yi: "A Zambiya yara ba sa iya zuwa makaranta saboda babu ruwa, amma ana iya canza hakan". Daukar ruwa aikin mata ne da yara, inda babu famfo da za a kunna kuma babu rijiya da za a ja daga ciki, dole ne a je wajen da za a dauko ruwa kafin a yi amfani da shi. Ko domin a sha, ko wanke-wanke ko kuma dafa abinci. Dole ne a dauki lita da yawa kowace rana, a cikin garwa da bokiti cikin yanayi na zafi a Zambiya.
Duk wanda ke da shekaru takwas zuwa sama, dole ne ya dauki ruwa zuwa Makarantar Al'umma ta Mangaba da safe. Kananan yara na daukar lita biyu da rabi, yayin da manya kuma ke daukar lita biyar. Karancin ruwa domin biyan bukatu na yau da kullum dai, yana shafar rayuwar yaran da ma karatunsu. Wasu kan kauracewa makaranta, saboda sai ka je da wuri za ka samu wurin zama a kan benci. Sai dai masu nazari na ganin cewar, gwamnati na iya sauya wannan lamari ta hanyar samar da rijiyoyin burtsatse isassu a wadannan yankuna.