1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar za ta zama sansanin yaki da ta'adda

Usman Shehu Usman MNA
April 22, 2022

Batun girke sojojin Jamus a Nijar da tura masu neman mafakar siyasa a Birtaniya kasar Ruwanda da ambaliyar ruwa a Afirka ta Kudu sun dauki hankalin jaridun Jamus.

Nijar | Sansanin 'yan gudun hijira a Ouallam | Ziyarar Annalena Baerbock
Hoto: Richard Walker/DW

Za mu fara da jaridar Die Tageszeitung, inda ta duba batun jibge sojojin Jamus a kasar Nijar. Jaridar ta ce bai kamata kasashen yamma su maimaita abin da ya faru a Afganistan ba, wato a ce sun gaza. Yanzu da suka samu sabani da kasar Mali, Nijar ta zama babban sansanin dakarun yaki da ta'addanci na kasashen waje a yankin Sahel. Sai dai wannan ba wata kyakkyawar shawara da za a yi maraba da ita ba. Domin hatta shi kanshi ministan harkokin wajen Nijar an jiyo shi yana mai cewa akwai alamu ta'addanci a nan gaba karuwa ma zai yi. Abin da ke a zahiri dai ga duk wanda ke son yin nasara a yaki da ta'addanci a yankin Sahel, to dole ya samu horon iya zama cikin hamada mai zafin gaske, kamar wanda yanzu haka sojojin Jamus ke yi. A gefen sansanin sojojin na Jamus da ke yankin Tillia a kasar Mali, 'yan kilomitoci ta bangaren Nijar akwai rundunar sojan Nijar ta musamman da ke da sansani. A wannan yankin dai babu titin mai kwalta da ake iya bi, amma kuma akwai wani filin jirgin sama da jiragen soja kan iya sauka, wanda rundunar sojan Jamus kan iya amfani da shi. A cikin makwannin nan dai ministar tsaron Jamus da ta harkokin waje, duk sun kai ziyara a Nijar da Mali kan batun na mayar da sojan Jamus daga Mali zuwa Nijar.

Ministar cikin gidan Birtaniya Priti Patel da ministan harkokin wajen Ruwanda Vincent Biruta, lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar taimakon tattalin arziki da raya kasaHoto: Muhizi Olivier/AP/dpa/picture alliance

Ruwanda za ta kasance kasar da mai bukatar mafakar siyasa a Birtaniya zai mika bukatarsa. Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce, a yanzu 'yan ciranin Afirka da ke Birtaniya wadanda ba su da izinin zama za a kwaso su daga London a dawo da su Ruwanda. A cewar firaministan Birtaniya kasar Ruwanda ita ce suka ga ta dace da jibge mutanen wanda daga nan za a duba takardunsu, in har sun cike sharuddan samun mafaka sai a basu. Boris Johnson ya ce kasar ita ce tafi zaman lafiya a Afirka. Kasar Birtaniya dai ta biya miliyoyin kudi ga kasar Ruwanda kan wannan yarjejeniyar, to amma fa shawarar wani mummunan koma baya ne ga dubban 'yan Afirka, wadanda da ma can talauci ne ya sa suka baro kasashensu, kuma yanzu an sake jibge su a wata 'yar mitsitsiyar kasa da ke tsakiyar Afirka.

Ambaliyar ruwa ta yi mummunar barna a Afirka ta Kudu. A nan wata gada ce da ta ruguje sakamakon ambaliyatr a kusa da birnin DurbanHoto: ROGAN WARD/REUTERS

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta duba mummunar ambaliya da ta faru a kasar Afirka ta Kudu ne. Jaridar ta ce bayan rugujewar gidaje biyo bayan ambaliya a kasar, al'ummar kasar Afirka ta Kudu ba su yi imanin cewa gwamnatinsu da cin hanci ya yi wa katutu, za ta iya taimakonsu da komai ba. Al'ummar kasar na jin tsoron cewa duk kudin da za a ware kan agaza wa wadanda ambaliyar ta shafa, to kawai za su kare ne a aljihun shugabannin jam'iyyar ANC mai mulkin kasar, wadanda aka soasu da handamar dukiyar gwamnati. Jaridar ta ce a gabar ruwan Durban da kuma yankin KwaZuluNatal, gidajen talakawa da yawa suka rushe sakamakon ruwa mai karfi hade da iska da tabo, abin da ya haifar da wani bala'i, inda mutane da yawa suka rasa matsuguni.

Kyakkyawan iri na tabar wiwi zai iya sa kasar Malawi ta zama mai arziki. Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce kasar Malawi ita ce aka yi imanin ta fi tabar wiwi mai kyau a duniya. Wannan yana faruwa ne a daidai lokacin da kasashen duniya suke amincewa da amfani da ganyen wiwi a matsayin sinadarin hada magunguna. Sai dai mummunan abin shi ne, yadda da yawa cikin talakawan Malawi ba za su gani a kasa ba, illa kawai su ci gaba da zama cikin talauci.