Juyin mulki a Afirka ya dauki hankali
February 4, 2022Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta rubuta sharhi mai taken kasa ta gaba da juyin mulki ya girgiza ita ce Guinea Bisau, amma sojojin ba su yi nasara ba. Yunkurin juyin mulkin sojojin na Guinea Bisau ya zo ne mako guda bayan takwarorinsu na Burkina Faso sun kifar da gwamnati. Sojojin da ke gadin fadar shugaban kasa a Guinea Bisau, sun kwashe tsahon sa'o'i suna musayar wuta da masu yunkurin juyin mulkin. Yunkurin dai ya zo ne, a daidai lokacin da Shugaba Umaro Sissoco Embaló da ministocinsa ke tsaka da gudanar da taro a fadarsa.
Ita kuwa jaridar die Tageszeitun ta rubuta sharhinta ne kan barakar da ke tsakanin Mali da kungiyar Tarayyar Turai, inda Malin ta ce ba ta bukatar ganin wakilan EU a kasarta. Jaridar ta ce kora da Mali ta yi wa jakadan uwargijiyarta kasar Faransa, ya kawo mummunar baraka tsakanin Mali da kasashen EU. Akwai dai sojojin Faransa da wasu kasashen na EU jibge a Mali, inda suka ce sun shiga kasar ne domin taya gwamnati yaki da masu ikirarin jihadi da suka addabe ta.
Ambaliyar ruwa da ta yi mummunar barna a wasu kasashen kudancin Afirka, a cewar jaridar Neue Zürcher Zeitung. Jaridar ta ce a kasashen Namibiya da Madagaska da Malawi da Zimbabuwe, kimanin mutane 80 sun halaka sakamakon ambaliyar ruwa. Tun a farkon wannan makon ne dai wata mummunar gugawa mai suna "Ana" ta fara yin mummunar barna a kudancin da gabashin Afirka, kuma ta raunata mutane da daman gaske. Sau tari dai a kan samu matsalar ambaliyar ruwa ne a kasashen Afirka, sakamakon rashin magudanar ruwa masu inganci ko ma babu su gaba daya.