1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin sanin tabbas a kan makomar Burundi

Mohammad Nasiru Awal AH
June 12, 2020

Mutuwar shugaban Burundi Pierre Nkurunziza, da kashe kwamandan Al-Qaida a yankin Magreb da kuma batun fafutukar yaki da masu yi wa mata fyade a Najeriya wadannan sune batutuwan da suka dauki hankali a jaridun Jamus.

Burundi Agathon Rwasa kondoliert zum Tod von Pierre Nkurunziza
Hoto: DW/Antéditeste Niragira

Jaridar Die Tageszeitung. A labarin da ta buga mai taken "Jagora" ya mutu, rashin tabbas ga makomar Burundi, jaridar ta ce bayan mutuwar ba-zata ta Shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza, akwai barazanar fuskantar gwagwarmayar rike madafun iko. Ta ce shugaban mai shekaru 55 da ya kirkiri sabon mukamin "Babban Jagoran Kishin kasa" da burin ci gaba da samun angizo a fagen siyasar kasar bayan ya sauka, yanzu dai mutuwa ta raba gardama domin ba zai jagoranci wannan ofis ba. Yanzu bisa tanadin kundin tsarin mulki, shugaban majalisar dokoki ne Pascal Nyabenda zai karbi jan ragama. Ana yi masa kallon mai adawa da shugaban kasa mai jiran gado Evariste Ndayishimiye a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar da ke mulki. Wata majiya ma ta labarto cewa an nuna wa juna 'yar yatsa tsakanin mutanen biyu a zaman farko da mahukunta suka yi bayan mutuwar Shugaba Nkurunziza. Ba a san halin da kasar za ta shiga ciki bayan mutuwar babban jagoran ba. Burundi dai na da tarihin tashe-tashe hankula. 'Yan adawar kasar da suka tsere sun bayyana fatan daidaituwar al'amura a kasar. A nata bangare gwamnati ta yi kira ga 'yan kasar da su kwantar da hankalinsu.

Har yanzu da sauran rina a kaba a yankin Sahel duk da cewar an kashe kwamanda Al-Qaida a yankin  Magreb

Abdelmalek Droukdal kwamandan Al-Qaida a Magreb da Faransa ta kasheHoto: picture-alliance/dpa/AFP/T. Coex

Karshen Abdelmalek Droukdal, Faransa ta ba da sanarwar kashe kwamandan Al-Qaida a yankin Magreb yayin da ta'addanci ke bazuwa a yankin Sahel, wannan shi ne kanun labarin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta buga kan mutuwar Droukdal. A karshen makon jiya ministar tsaron Faransa Florence Parly ta ce sojojin kasar sun sami gagarumar nasara a yakin da ake yi da kungiyar ta'adda ta Al-Kaida a yankin Magreb. Tun a ranar Laraba ta makon jiya wata runduna ta musamman ta halaka Abdelmalek Droukdal a wani yankin kan iyakar kasar Mali da Aljeriya. Sai dai wasu masharhanta na cewa kashe kwamandan kungiyar a yankin na Magreb ba ya nufin an kawar da kalubalen ta'addanci a yankin Sahel.
Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi tsokaci kan wannan batu tana mai cewa kawar da daya daga cikin manyan jagororin 'yan jihadi a yankin Sahel, Abdelmalek Droukdal dan asalin kasar Aljeriya, ba shi ne karshen rigingimu a kasar Mali mai fama da matsalolin tashe-tashen hankula ba. Jaridar ta ce zai zama yaudarar kai a yi imanin cewa kawar da Droukdal daidai yake da murkushe kungiyar Aqmi, wato reshen Al-Kaida a yankin Magreb.

Mata a Najeriya na neman hukumomin da su ba rika hukunta masu aikata laifukan fyade

Hoto: DW/U. Abubakar

A karshe sai jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka Najeriya yayin da ake kara yin kira da daukar tsauraran matakai kan masu yi wa mata fyade a kasar. Jaridar ta ce kisan wata dailba 'yar shekara 22 bayan an yi mata fyade daya ne daga cikin wannan ta'asa da ke karuwa kusan a kullum a tarayyar ta Najeriya musamman lokacin dokar kulle da ke aiki saboda yaki da cutar COVID-19. Yanzu dai mata a Najeriya sun tashi tsaye don ganin an kawo karshen wannan ta'asa, suna masu kira ga mahukunta da su ba da kariya ga mata da sauran kananan yara da ke fuskanta wannan cin zarafi, kana kuma a hukunta masu aikata laifin