1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jaridun Jamus sun yi sharhi kan malariya

Abdullahi Tanko Bala LMJ
September 15, 2023

Kokarin sauya kwayar zazzabin cizon sauro domin sauron ya daina yada cuta da juyin mulki a Afirka da kuma kokarin Jamus na inganta dangantaka da Afirkan, sun dauki hankulan jaridun Jamus.

Sauro | Cizo | Zazzabi | Malariya | Hana Tasiri
Ko za a cimma nasarar hana sauro yada zazzabin malariya musamman a Afirka?Hoto: pzAxe/IMAGO

A sharhinta mai taken shin za a iya sauya kwayar hallitar cutar zazzabin cizon sauro, yadda sauron ba zai iya yada cutar ba? Jaridar die tageszeitung ta ce ana wani bincike na kasa da kasa a kan wannan batu. Zazzabin cizon sauro dai na da matukar sosa rai, inda a wasu sassan duniya ya kan kai ga halaka mutane masu yawa. Kwayar cutar malariya da macen sauro ke yadawa an fi samunta musamman a Afirka, inda lamarin ya fi kamari. A shekarar 2020 mutane kusan dubu 600 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar. Jaridar ta die tageszeitung ta ce a kasar Yuganda  kadai, an yi kiyasin cewa a cikin mutane miliyan 13 da suka kamu da cutar malaria dubu 20 sun mutu.

Jonathan Kayondo masanin hallitar kwari da ke cibiyar binciken kwayoyin cutattuka a Yuganda ya ce burinsu shi ne inganta yanayin sauron yadda ba zai iya yada cutar Malariya ba. Gudanar da wannan aiki ya kasu kashi biyu na farko a tsara yanayin jerin kwayar hallitar RNA da kuma jirkita kwayar hallitar DNA. A nan gaba al'umma za su sami sauki daga wannan cuta saboda an jirkita kwayar hallitar sauron, namijin da kuma ta matar  yadda ba za su iya haihuwa ba. Ta matar ba zata iya yin kwai ba ballatana su kyankyashe. Don haka ba za su iya cizo ko shan jini ba.

Taron Turkiyya da Afirka karo na uku a 2021Hoto: Emrah Yorulmaz/AA/picture alliance

Turkiyya na amfana a asirce daga juye-juyen mulki a yammacin Afirka. Wannan shi ne taken sharhin jaridar Neue Zürcher Zeitung. Jaridar ta ce a karkashin mulkin Shugaba Racep Tayyip Erdogan Ankara na fadada tasirinta a Afirka, domin maye gurbin Faransa da ke fsukantar turjiya a wasu kasashen da ta yi wa mulkin mallaka. Jaridar ta yi nuni da cewa a lokacin da sojoji suka kwace mulki a watan Augustan 2020 a Mali, cikin makonni uku kacal ministan harkokin wajen Turkiyya na wancan lokaci Mevlut Cavusoglu ya kai ziyara ya kuma gana da sababbin mahukuntan Malin a Bamako. A saboda haka Turkiyya ta zama kasa ta farko wadda a fakaice ta amince da halascin sojojin da suka yi juyin mulki yayin da Kasashen Yamma musamman kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO da kuma Faransa suka rika sukar lamirin.

A game da dambarwar Burkina Faso kuwa a 2022 da kuma Jamhuriyar Nijar a watan Yulin da ya gabata, ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta mayar da martani ne ta hanyar diflomasiyya tana taka-tsantsan. Haka ma a Gabon makonni biyun da suka wuce, inda sojoji suka kwace mulki. Ankara ta rika bin lamarin da idon basira tare da fatan zaman lafiya da kwanciyar hankali za su dore. Wannan ya sa manazarta ke cewa akwai yiwuwar Turkiyya za ta fi amfana daga hargitsin da ke faruwa a Sahel ta fuskar tattalin arziki da manufofin kawancen hadin gwiwa da ma na taimakon jinkai. A waje guda kuma kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da Najeriya, wani babban tagomashi ne ga Ankaran.

ministar raya kasashe ta Jamus Svenja Schulze yayin ziyarata a NajeriyaHoto: Leon Kuegeler/photothek.de/IMAGO

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yiwa sharhinta taken: 'Yan ta'adda ba sa gina bututun ruwa, ta yi tsokaci kan jawabin ministar raya kasa ta Jamus Svenja Schulze da ta jadddada bukatar kasashen Turai su kara kaimi a huldarsu da Afirka musamman a cinikayya. Schulze dai ta kai ziyara yammacin Afirka a 'yan kwanakin nan, kuma babban makasudi shi ne juyin mulkin Nijar. Jaridar ta ce idan aka dubi karuwar rashin kwanciyar hankali a Yankin Sahel, ana iya cewa daukacin yankin na tangal-tangal. Kaso 60 cikin 100 na al'ummar yankin, matasa ne 'yan kasa da shekaru 25 da haihuwa. A saboda haka abu ne da zai yi tasiri idan aka yi nazari wajen taimaka wa yankin da matasan manyan gobe, domin dorewar zaman lafiya da ci-gaba ko da yake a NIjar babu halastacciyar gwamnati da za a zauna a tattauna da ita a cewar jaridar.