Fargabar corona a yankuna da ake rigingimu
June 5, 2020Neue Zürcher Zeitung: Yara masu gararanba a titi
Saboda dokar hana fita da aka kafa ta jefa rayuwarsu cikin wani yanayi, inda suke buya domin gudun fadawa hannun jami'an 'yan sanda. Basa iya yin bara, saboda kowa na gudunsu. Akan haka ne kungiyoyi masu zaman kansu da gwamnati suka fara fafutukar ganin wadannan yara sun koma karkashin iyayensu ko kuma an samar musu mafaka.
Sai dai matsalar wadda ke da alaka da addini na da sarkakiya, ganin cewar mafi yawa daga cikinsu sun fito karatun allo ne a karkashin malamai na addini, wadanda kuma ke turasu yin bara da rana.
Iyayen akasarin irin wadannan yaran dai talakawa ne wadanda ke ganin cewar tura yaran zuwa neman ilin addini, tamkar wata dama ce da yaran zasu samu ilimin addini, a daya hannun kuma sun huta da kulawa dasu. Sai dai Covid-19, ta sa gwamnatocin kasashen Afirka da abun ya shafa sun fara daukar matakai da a baya suka gaza.
Süddeutsche Zeitung: " Corona da aikin rundunar tsaron Jamus a ketare
Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi " Corona ta shafi ayyukan rundunar tsaron Jamus ta Bundeswehr da ke aiki a ketare".
Jaridar ta ce akwai fargabar yaduwar cutar corona a wasu yankuna da ke fama da rigingimu. Jaridar ta kara da cewa ya kamata a kara yawan sojojin Jamus da ke kasar Mali a yankin yammacin Afirka. A 'yan kwanakin da suka gabata, majalisar dokokin Jamus ta amince da kudurin.
Sojojin Bundeswehr na Jamus din 450 za a tura zuwa Mali, a wani mataki na fadada ayyukan horon da sojojin Turai da ke fada da kungiyoyin tarzoma a yankin Sahel. Hakan na nufin karin dakaru 100 fiye da yadda lamarin yake a baya.
A yanzu haka dai an dakatar da ayyukan horo da dakarun ke bayarwa, sakamakon annobar Covid 19 da duniya ke fama da ita, ciki har da wadannan kasashe da ke fama da rigingimun 'yan tawaye.
die Taggesspiegel: Yaki da corona a Afirka
A nata bangaren jaridar die Taggesspiegel tsokaci ta yi game da bukatar kasashen Afirka su mike wajen yaki da annobar corona kamar yadda sauran kasashe da suka cigaba ke yi, duk da cewar cigaban na'urar zamani bai kai wannan nahiyar ba. Wajibi ne mutane su bada tasu gundummowa a fafutukar kawar da cutar.
Jaridar ta cigaba da cewar, sai bayan watanni uku da bullar annobar ce dai, corona ta isa Afirka. A bayan nan ne kowace rana ta zame tamkar sabon babi a rayuwar al'ummarta.
To sai dai bayan corona, akwai wasu muhimman batutuwa da Afirka ke fuskanta, cikinsu akwai zabbuka da kuma farfado da tattalin arzikinta. Kada a manta mutum na farko da ya shigar da cutar corona nahiyar Afirka dai daga Turai yake.