1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ruwanda da Sudan cikin jaridun Jamus

Abdullahi Tanko Bala
April 5, 2024

Kisan kiyashi a Ruwanda da batun hauren giwaye a Botswana da halin da ake ciki a Sudan da kuma samun mace firaminista a karon farko a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango suna jaridun Jamus.

Hotunan wasu daga iyali guda da aka kashe kisan kiyashin Ruwanda a 1994
Hoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

Jaridar Welt Online, ta yi sharhinta kan shekaru 30 da kisan kiyashi a Ruwanda. Ta ce yayin da ake jimamin wannan abin bakin ciki da ya faru abin dubawa shine yadda jama'a suka nuna hakuri da juriya tare da yafe wa juna, inda ake zaune lafiya tsakanin wadanda suka aikata ta'asar da kuma wadanda aka aikatawa. Bayan shekaru 30 a shekara mai zuwa za a sako wasu da aka samu da wannan laifi da aka daure a gidan yari, sai dai abin tambaya shi ne mai zai faru bayan nan ? yaya iyalai da al'umma a kauyuka za su ji? mutane kimanin 800,000 aka kashe a wannan ta'asa. Gwamnatin Shugaba Paul Kagame na fatan sakin dubban fursunonin, domin karfafa sasantawa a tsakanin al'umma da sajewa cikin al'amuran rayuwa da kuma rage cinkoso a gidajen yari.

Botswana za ta bai wa Jamus kyautar giwayeHoto: ARTUSH/Zoonar/picture alliance

Shagube na kyautar giwaye 20,000 da shugaban Botswana ya ce zai bai wa Jamus shi ne ya dauki hankalin jaridu da dama a Jamus da suka hada da Der Tagesspiegel da WeltPlus da Neue Zürcher Zeitung da Bild da dai sauransu. Wannan dai jurwaye ne mai kamar wanka ko kuma hannunka mai sanda Botswana ta yi wa gwamnatin Jamus wadda ta nuna adawa da safarar hauren giwa a cewar die Bild. Jaridar ta ce tsokana ce da gangan shugaban Botswana Mokgweetsi Masisi ya yi ga gwamnatin Jamus inda ya ce idan ba ku son haure, to za mu ba ku giwayen 20,000 su wataya ku ga abin da suke dauke da shi, sannan ya kamata Jamusawa su koyi zama tare da giwaye.

Yakin Sudan na ci gaba da tarwatsa al'ummar kasarHoto: David Allignon/MAXPPP/dpa/picture alliance

Walau Gaza ko Sudan kasashen Turai da sauran kasashen duniya sun kau da kai daga halin da ake ciki. Wannan shi ne taken sharhin jaridar die tageszeitung. Jaridar ta ce a bisa alkaluman Majalisar Dinkin Duniya, fiye da kashi daya cikin kashi uku na al'ummar Sudan miliyan goma sha bakwai da dubu 700 suna fama da karancin abinci. Kimanin mutane miliyan hudu na fama da tamowa yayin da wasu miliyan tara suke gudun hijira a ciki da wajen kasar. Wasu da ke kan iyaka da kasar Chadi ba su da komai, kungiyoyin agaji da ke taimaka musu ba su da kudi, yayin da a waje guda duniya ta sa ido kan ta'asar da faruwa a Gaza, bala'in da ake ciki a Sudan bai dauki hankalin manyan kasashen ba, shekara guda bayan barkewar wannan yaki. Wanda zai iya guduwa ya gudu wanda ba zai iya ba kuma sai dai ya mutu.

Firaminista mace ta farko a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Xinhua News Agency/picture alliance

A karon farko mace ta zama firaminista a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Jaridar die Tageszeitung ta ce Judith Suminwa Tuluka wadda ta rike mukamin ministar tsare-tsare tana daga cikin amintattun shugaban kasar Felix Tshisekedi. A yanzu dai sabuwar firaministar na da gagarumin kalubale na kafa sabuwar gwamnati. Nadin na ta a kan mukamin na zuwa ne makonni shida bayan murabus din tsohon firaminista Augustin Kabuya da ya ajiye a ranar 20 ga watan Fabrairu. Mai shekaru 56 da haihuwa, ko yaya karfin tasirinta zai kasance a cikin gwamnati lokaci ne zai nuna.