1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Siyasar Gambiya da bore a Kamaru

Mohammad Nasiru Awal
February 1, 2017

A wannan makon siyasar kasar Gambiya da halin da ake ciki a yankin da ke amfani da harshen ingilishi a kasar Kamaru sun dauki hankalin jaridun na Jamus.

Gambia's new President Adama Barrow
Hoto: picture alliance/abaca/X.Olleros

A labarin da ta buga mai taken wanda ya yi nasara ya koma gida, jaridar Die Tageszeitung cewa ta yi:

Zababben shugaban kasar Gambiya Adama Barrow na cike da murna. Ta ce ba a zaben ranar daya ga watan Disamban 2016 kawai ya yi nasarar kawar da tsohon shugaban kasar da ya kwashe shekaru da yawa a kan mulki ba, a'a yanzu Barrow ne shugaban kasa na hakika. Jaridar ta ce Barrow da a matsayin na farko a tarihi na sauyin mulki na demokradiyyar a Gambiya, ya kuma kasance dan Afirka na farko da ya yi zaman ci-rani a Turai amma ya koma gida ya zama shugaban kasarsa. Barrow wanda ya koma birnin Banjul bayan da Yahya Jammeh ya mika wuya ga matsin lamba daga kasashen ECOWAS, ya yi alkawarin sake gina kasar ta Gambiya a kan turba ta gaskiya da adalci.

Shin za a iya gurfanar da Jammeh gaban ICC?

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tsokaci ta yi game da kasar Equitorial-Guinea wadda ta ba wa tsohon shugaban Gambiya Yahya Jammeh mafaka.

Hoto: picture-alliance/AP/dpa/J. Delay

Ta ce Jammeh ya zabi zuwa Equitorial-Guinea bayan da iyalan Obiang da ke mulki a kasar suka ba shi mafaka. Sai dai akwai ayar tambaya game da wannan zabi, domin duk da yarjejeniyar da aka kulla cewa ba za a iya farautar Jammeh da mukarrabansa ba, a ranar Litinin shugaban hukumar kungiyar ECOWAS Marcel de Souza ya ce doka ba ta tilasta aiki da yarjejeniyar ba. To sai dai koda ECOWAS da tarayyar Afirka za su canja matsayinsu, suka nemi da a gurfanar da Jammeh gaban kotu, to da wuya domin Equitorialo-Guinea ba ta amince da kotun duniya ta ICC ba kana kuma ba ta kulla wata yarjejeniyar tasa keyar wani da wata kasa ba.

Boren adawa da manufar gwamnatin Kamaru

Masu magana da harshen ingilishi a Kamaru suna boren adawa da babakeren da masu magana da faransanci suka yi musu inji jaridar Neue Zürcher Zeitung, sannan sai ta ci gaba tana mai cewa:

Hoto: Moki Kindzeka

Tun wasu watanni ke nan takaddama kan harsuna ta raba kan 'yan Kamaru. Ta ce Kamaru kamar kasar Kanada suna da yankuna na masu magana da harshen faransanci da na masu magana da harshen ingilishi. To amma a Kamaru masu amfani da faransanci ke da rinjaye, yayin da kashi 20 cikin 100 na al'ummar kasar kimanin miliyan 22 ne 'yan anglophone da suka dade suna korafi ana nuna musu wariya a fannoni dabam-dabam na rayuwa ci gaban kasa. Dalili ke nan da ya sa su gudanar da zanga-zanga da yajin aiki suna kalubalantar gwamnatin tsakiya da aiwatar da mulkin kama karya a kansu.