1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Sudan da Kamaru sun dauki hankali

Mohammad Nasiru Awal MA
August 23, 2019

Siyasar Sudan da Kamaru batutuwa ne da suka kasance manya a shafukan jaridu dangane da abubuwan da suka wakana a Afirka a mako. Jaridun Jamus ma sun nazarce su.

Sudan Abdel Fattah al-Burhan, Chairman Transitional Military Council (TMC)
Janar Abdel Fatta al-Burhan, shugaban majalisar riko a SudanHoto: Imago Images/Xinhua

A labarin da ta buga mai taken Sudan ta hau hanyar girke mulkin dimukuradiyya jaridar Die Tageszeitung ta fara ne da cewa: bayan kifar da gwamnatin shugaban mulkin kama karya, yanzu wata majalisa mai wakilai 11 za ta jagoranci kasar bayan kawo karshen zamanin al-Bashir. Ta ce bayan da a karshen makon jiya kawancen 'yan adawa da sojojin suka amince da yarjejeniyar raba madafun iko, a ranar Laraba aka rantsar da shugaban majalisar rikon kwarya, Janar Abdel Fatta al-Burhan, da ya rike madafun iko tun bayan hambarar da tsohon shugaban kasa Omar al-Bashir a cikin watan Afrilu da ya gabata.

Jaridar ta ce ba ta sauya zani ba a dangane da jagororin, amma sabon abu sh ne majalisar rikon da ke matsayin gwamnatin kasar a yanzu ta kunshi fararen hula shida ciki har da mace daya da kuma sojoji biyar da za su ja ragama tsawon watanni 21 sannan su mika wa farar hula su ma su nuna kamun ludayensu tsawon watanni 18, kafin a gudanar da zabuka. Jaridar ta yaba da wannan tsarin tana mai cewa ya hana a yi mummunar arangama tsakanin sojoji da 'yan adawa. Sai dai ayar tambaya a nan ita ce ko Janar-Janar din da suka kwashe shekaru 30 suna jan akalar kasar za su yarda su yi bankwana da madafun iko?

Tsohon Shugaba al Bashir a KotuHoto: Getty Images/AFP/E. Hamid

Ita ma jaridar Berliner Zeitung ta yi tsokaci kan halin da ake ciki a Sudan din sai dai ta mayar da hankali ne kan shari'ar da aka fara yi wa tsohon shugaban kasa Omar al-Bashir a ranar Litinin da ta gabata, tana mai cewa zargin da ake masa shi ne na wawashe dukiyar kasa.

 

Daurin rai da rai ga 'yan aware wannan shi ne taken labarin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta buga a tsokacin da ta yi na halin da ake ciki a yankin masu amfani da harshen Ingilishi na kasar Kamaru. Jaridar ta ruwaito wani lauyan kare hakkin dan Adam na cewa hukuncin daurin rai da rai a kurkuku da wata kotun soji da ke birnin Younde ta yanke wa mutane 10 da ke zama jagororin 'yan adawa bisa laifin aikata ta'addanci da ayyana 'yancin kan yankin da suka kira kasar Ambazoniya ba zai taba magance matsalolin Kamaru ba.

Jami'an tsaro a KamaruHoto: Getty Images/AFP

Tsawon shekaru al'ummar yankin na masu amfani da Ingilishi ke bore na adawa da mayar da su saniyar ware da gwamnatin tsakiya masu amfani da Faransanci ta yi, lamarin da ya janyo asarar rayuka kimanin dubu biyu sannan wasu rabin miliyan suka tsere daga yankunansu na asali. Ganin har yanzu rikicin ya ki ci ya ki cinyewa, kamata ya yi sassan biyu su nemi hanyoyin sasanta rikicin cikin lumana.

Har yanzu dai halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango musamman kan cutar Ebola na ci gaba da daukar hankalin jaridun Jamus. A sharhin da ta yi kan batun jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi abokin gaba da na ba a ganinshi, sannan sai ta kara da cewa a yankin Arewa maso Gabashin Kwango likitoci na ci gaba da yaki da cutar Ebola, to sai dai ba kwayoyin cutar ne kadai ke da hatsari ba, ayyukan kungiyoyin 'yan tawaye a yankin na kara janyo babban cikas ga kokarin shawo kan annobar ta Ebola.