1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Chadi ya dauki hankalin jaridun Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afar SB
May 10, 2024

Zaben kasar Chadi gami da shirye-shiryen zaben kasar Afirka ta Kudu a karshen wannan wata na Mayu suna daga cikin abubuwa da jaridun Jamus suka mayar da hankali.

Shugaba Mahamat Deby Itno na Chadi
Shugaba Mahamat Deby Itno na ChadiHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Zaben shugaban kasa a kasar farko da aka yi bayan juyin mulki a Afirka, in ji jaridar Neue Zürcher Zeitung. Jaridar ta ce Chadi ta gudanar da zaben shugaban kasa, wanda ake sa ran dan tsohon shugaban kasar mulkin kama-karya na mutu ka raba da ke zaman abokin Amurka da Faransa ne zai lashe. Jaridar ta ce a wasu yankunan an samu karancin fitowar masu kada kuri'a, duk da cewa kimanin mutane miliyan takwas da dubu 500 ne suka cancancin yin zaben a kasar da ke yankin Sahel. An raba takardu dauke da sunan 'yan takara da mace daya tilo ke cikinsu ne ke neman zama shugaban kasa a Chadin da fadin kasarta ya ninka Jamus har sama da sau uku, wadda kuma kalubalen da ke jiran sabon shugaban kasar da za a zaba ke da tarin yawa fiye da girmanta. Kama daga rashin aikin yi da tashe-tashen hankula a wasu yankunan kasar da rikice-rikice a kasashe makwabta musamman ma daga Sudan, inda a yanzu sama da 'yan gudun hijirata dubu 750 ke neman mafaka a Chadin.

Firamnista Succes Masra na kasar ChadiHoto: Issouf Sanogo/AFP

Karin Bayani: Labaran Afirka masu daukar hankali a jaridun Jamus

Ita kuwa jaridar die tageszeitung ta rubuta sharhinta ne mai taken, zargi a kan babbar abokiyar hamayyar jam'iyyar ANC. Zargin sa hannu na bogi da satar suna ya kassara sabuwar jam'iyyar MK ta tshohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma. Jaridar ta ce: Jam'iyyar MK da ake wa kallon babbar barazana ga takwararta ta ANC mai mulki a yanzu ta samu kanta a rikicin cikin gida, inda har guda daga cikin wadanda suka kafata Jabulani Kumalo ya nemi hukumar zaben kasar da ta cire sunan tsohon shugaban kasar Zuma a matsayin shugaban jam'iyyar ta MK domin mukamin nasa ne.

Jacob Zuma tsohon shugaban kasar Afirka ta KuduHoto: AP/picture alliance

Bayan jerin kararraki da ta fuskanta a kotu sakamakon satar sunan tsohon bangaren soja na jam'iyyar ANC mai mulkin, guda daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar ta MK da aka kora ya ba da shaidar cewa wasu daga cikin sanya hannu na mutane dubu 15 da ake bukata kafin amince mata ta shiga zaben shugaban kasar na bogi ne. Zargin da ake wa sabuwar jam'iyyar ta MK ya nunar da cewa, masu fafutuka na MK din sun saci sanya hannu wadanda ke neman aiki ne ba tare da amincewarsu ba. Daga bisani sun yi amfani da sunayensu da adireshinsu, kafin su mika ga hukumar zaben kasar domin samun damar shiga a fafata da su a zaben. Tuni dai 'yan sandan Afirka ta Kudun suka tabbatar da cewa suna gudanar da bincike a birnin Cape Town, inda a nan ne aka shirya wannan badakala.

Barka da zuwa RuwandaHoto: Stephanie Aglietti/AFP/Getty Images

Jaridar WELTplus ta rubuta mai taken: Daddumar salla da Abincin Halal-yadda Ruwanda ta shirya karbar 'yan gudun hijira. Ta ce a Ruwanda, ana sa ran nan ba da jimawa ba ne rukunin farko na masu neman mafaka da Birtaniya za ta mayar Afirka za su isa Kigali. Ziyarar da aka kai masaukin da ake shirin ajiye su, ya nuna yadda kasar ta dauki abun da muhimmanci. Ba wai batun makudan kudin da za a kashe ba ne kawai, Ruwanda na yi wa London alfarmar saboda wani dalili na dabam. Jaridar ta ce a kofar masaukin 'yan gudun hijira na "Hope Hostel" an kafe rubutun da ke dauke da "ka zo a matsayin bako, ka koma a matsayin aboki", wadannan su ne kalamai na farko da za su yi wa masu neman mafakar rukunin farko da Birtaniya ta fatattaka zuwa Ruwanda a karkashin wata yarjejeniya da suka kulla duk kuwa da cewa ba sa son komawa Kigalin maraba. Tsawon shekaru biyu ke nan ana ta kiki-kaka dangane da batun mayar da masu neman mafakar zuwa Ruwanda, inda kotuna da dama a Birtaniyan suka yi kokarin dakilewa sakamakon fargabar da ake na yanayin yadda gwamnatin Kigalin ke gudanar da al'amuranta kan masu neman mafaka. Sai dai a watan Afrilun da ya gabata, 'yan majalisar dokokin Birtaniyan sun amince da wani kudirin doka da ya yadda a mayar da masu neman mafakar na Ingila zuwa kasar da ke yankin gabashin Afirkan.