1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin Rasha a Afirka cikin jaridun Jamus

Abdullahi Tanko Bala LMJ
June 3, 2022

Tairin rikicin Rasha da Ukraine kan nahiyar Afirka da kuma hadin kan Musulmi a kasar Senegal, sun dauki hankulan jaridun Jamus na wannan makon.

Odesa Hafen
Miliyoyin ton na hatsi ne dai, jibge a tashoshin jiragen ruwan UkraineHoto: imago images/unkas_photo

Za mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung a sharhinta mai taken bukatar gaggawa ta lalubo sababbin hanyoyin safarar kayayyaki. Jaridar ta ce sakamakon mamayar Ukraine, Kyiv na fatan fitar da hatsinta ta jirgin kasa. Ana dai fama da karancin hatsi a arewacin Afirka da Gabas ta Tsakiya, yayin da a waje guda hatsin ke makare a Ukraine. Dalilin hakan dai shi ne datse tashar jiragen ruwan Ukraine ta gefen Baharul Aswad, inda Kiev ke fitar da fiye da kaso 90 cikin 100 na hatsinta kafin barkewar yakin. A yanzu Ukraine da kawayenta na kasashen Turai, sun kagu wajen neman mafita. Domin kare fuskantar matsalar yunwa a Afirka da Gabas Ta Tsakiya da kuma kokarin cika rumbun ajiya kafin kakar badi, akwai bukatar fitar da ton miliyan 20 na hastin kafin karshen watan Yuli. Ukraine din dai na fatan fitar da hatsin ne ta hanyoyin mota da jirgin kasa da kuma ruwa ta kogin Danube. Sai dai kuma wani tarnaki shi ne, karancin taragan jiragen kasa. Kama daga hanyoyin jiragen kasar Ukraine da kamfanonin jiragen kasa na kasashen Turai, babu wadanda suke da tsarin da zai iya jigilar hatsi mai tarin yawa kamar haka. Domin hanzarta safarar hatsin, Hukumar Tarayyar Turai ta gabatar da shirin samun hadin kai a hanyoyi yadda jiragen za su wuce ba tare da jinkiri ba musamman saukaka tarnaki wajen jami'an Hukumar Hana Fasa Kwabri.

Rasha ta jima tana kokarin karfafa hulda da kasashen AfirkaHoto: SERGEI CHIRIKOV/AFP

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a nata bangaren, ta yi sharhi ne kan sassauta burin Rasha na kafa tashoshin nukiliya a Afirka. Jaridar ta ce ayyukan da Rasha ta sa a gaba a Afirka, sun samu cikas tun farkon farawa. Wannan shi ne babban batu a jadawalin taron koli tsakanin Afirka da Rasha a birnin Sochi. Rasha na fatan farfado da tasirinta a Afirka tun a 2019, ta hanyar gina tashoshin nukiliya. An rattaba hannu a kan yarjeniyoyi na kafa cibiyoyin lumana na makamashin nukiliya, ciki har da kasashen Ruwanda da Yuganda da Habasha. Jaridar ta ce gwamnatoci da dama na Afirka na dari-dari wajen sukar lamirin Rasha, inda suka kasance baina-baina ko kuma masu bin tafarkin Rasha. Sai dai kuma duk da haka yakin Ukraine na iya rage kaifin tasirin Rasha, saboda raunin karfin tattalin arzikinta sakamakon jerin takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata. Yayin da a waje guda Rashar ta dogara ga yammacin Turai, wajen muhimman fasahohi na gina tashar nukiliya.

Shugaban darikar Tijjaniya a Senegal Ibrahim Niass (C) tare ad Shugaba Macky SallHoto: picture-alliance/AA/A. Gueye

Ita kuwa Jaridar die tageszeitung, ta yi sharhi ne a kan tasirin hadin kan 'yan uwa Musulmi a Senegal. Jaridar ta ce, babu inda mabiya darikar sufaye suke da hadin kai da karfin tasiri a tsakanin al'umma da kuma siyasa kamar kasar Senegal. Jaridar ta ce watakila wannan shi ne dalilin da ya sa, 'yan ta'adda masu fakewa da addini ba su samu gindin zama a kasar ba. Kimanin kaso 95 cikin 100 na 'yan kasar miliyan 18 Musulmi ne, baya ga mabiya darikar sufaye akwai kuma 'yan Tijjaniyya da 'yan Kadiriyya wadanda suke da magoya baya da dama. Saboda tasirin addini a tsakanin al'umma, duk mai son samun nasarar zabe a Senegal sai ya samu hadin kan 'yan brotherhood musamman mabiya darikar sufaye da suka kasance masu rinjaye wadanda su ne ke juya akalar inda kasar ta dosa.