1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Senegal da Mozambik a Jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar LMJ
March 8, 2024

Halin da ake ciki a Senegal da Mozambik da kuma batun mayar da 'yan gudun hijira zuwa Ruwanda daga Birtaniya sun dauki hankalin jaridun Jamus

Afirka a Jaridun Jamus | Sharhi | Senegal | Siyasa
Rikicin siyasar Senegal cikin jaridun JamusHoto: Cem Ozde/Anadolu/picture alliance

Jaridar Zeit Online ta wallafa sharhi mai taken "Senegal ta sanya sabuwar ranar gudanar da zaben shugaban kasa". Jaridar ta ce kammala wa'adin shugaban Senegal Macky Sall ya sa ba zai iya sake tsayawa takara ba, a karkshin tanadin kundin tsarin mulkin kasar ta yammacin Afirka ba. A dangane da haka ya yi kokarin dage ranar zaben, matakin da ya saba wa tsarin mulkin kasar. Yanzu dai an tsayar za gudanar da zaben a karshen watan Maris, inda majalisar tsarin mulkin kasar ta Afirka ta Yamma ta yanke shawarar cewa dole ne a gudanar da zaben kafin ranar biyu ga watan Afrilun da ke tafe gabanin kammala wa'adin mulkin Sall maimakon biyu ga watan Yunin da shugaban kasar ya gabatar mata tun da farko kafin ya dawo 24 ga wannan wata na Maris a matsayin ranar da za a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasar ta Senegal.

Jami'an tsaro na fafutukar ganin sun kori 'yan ta'adda a MozambikHoto: DW

"Wani sabon tashin hankali a Mozambik" da haka ne jaridar die Tageszeitung ta bude labarin da ta rubuta a kan sabon harin da masu tayar da kayar baya na Mosambik da dakarun shiga tsakani daga kasashen Ruwanda da Afirka ta Kudu suka fatattaka a shekarar 2021 suka kai. Janyewar da sojoji daga kudancin Afirka ke yi, ya kara musu kwarin gwiwa wajen kaddamar da sababbin hare-hare. Wannan rikici da ya lafa na wani lokaci, ya sake kunno kai. Tun daga watan Fabrairun da ya gabata, fiye da fararen hula dubu 70 ne suka tsere daga matsugunnansu sakamakon sababbin hare-hare a arewacin kasar. Bayan nasarorin farko da aka samu, ga dukkan alamu dakarun shiga tsakani na kasar Ruwanda da na kungiyar Raya Kasashen Kudancin Afirka (SADC), sun kasa shawo kan boren kungiyar 'yan ta'addan da ake kira "Ahlu Sunnah Wal jama'a da ta addabi kasar ta Mozambik.

An dade ana cece-kuce kan mayar da 'yan gudun hijira daga Birtaniya zuwa RuwandaHoto: House of Commons/UK Parliament//PA Wire/empics/picture alliance

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta wallafa na da sharhin ni kan halin tsaka-mai-wuya da kudirin dokar mayar da 'yan gudun hijira daga Birtaniya zuwa kasar Ruwanda ya fada ciki, a gaban majalisar dattijan kasar. Majalisar dokokin Birtaniyyan dai ta yi watsi da kudirin dokar wanda gwamnatin 'yan mazan jiya ke son yin amfani da ita, wajen korar 'yan gudun hijirar da suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba zuwa kasar Ruwanda da ke gabashin Afirka ba tare da 'yancin daukaka kara ba. Wannan dai shi ne karo na biyar da aka yi wa wannan kudiri gyaran fuska domin samun amincewa, tare da ayyana Ruwanda a matsayin kasar da za ta kasance ta uku mai aminci a fannin tsaro nan gaba matsayin da kotun koli a Londan ta nuna shakku a kansa.