1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: 'Yan tarzoma na ci da gumin kananan yara

Mohammad Nasiru AwalApril 15, 2016

Yayin da aka cika shekaru biyu da sace 'yan matan Chibok, Boko Haram na ci gaba da amfani da yara a matsayin 'yan kunar bakin wake.

Nigeria Befreite Geiseln Boko Haram
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus game da nahiyarmu ta Afirka da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda a wannan mako ta leka Najeriya a daidai lokacin da aka cika shekaru biyu da kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan makarantar sakandaren Chibok.

Ta ce yayin da daruruwan matan suka shafe shekaru biyu a hannun mayakan na Boko Haram, kungiyar na ci gaba da cin zarafin kananan yara tana amfani da su a matsayin 'yan harin kunar bakin wake. Jaridar ta rawaito wani rahoton asusun taimakon yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF na cewa yara 'yan shekarun haihuwa daga takwas Boko Haram ke yaudararsu suna kai harin kunar bakin wake a Najeriya da Kamaru da Chadi da kuma Nijar, kuma kashi uku cikin hudu 'yan harin kunar bakin waken 'yan mata ne.

Fadada aikin horas da dakarun tsaro

Har yanzu muna kan batun na tarzoma inda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce rundunar sojojin Jamus ta Bundeswehr ta fadada aikin horas da jami'in tsaro a kasashen yankin Sahel musamman a Mali.

Hoto: picture-alliance/dpa/M. Gambarini

Ta ce majalisar ministocin Jamus ta amince da kudurin tsawaita aikin rundunar sojin kasar a Afirka inda jaridar ta ce ko da yake an rage yawan sojojin daga 900 zuwa 600 amma hakan ba zai kawo tsaiko ga aikin da suke yi na horas da sojojin Mali karkashin inuwar tawagar sojojin tarayyar Turai ba. Yanzu haka sojojin na Turai sun horas da takwarorinsu na Mali kimanin 8000 dubarun yaki dabam-dabam da kuma kai dauki cikin gaggawa. A halin da ake ciki za a fadada yankin horaswa inda ya kunshi ilahirin yankunan kan iyakar Mali da kasashe makwabta.

Demokradiyya ko mulkin danniya?

Shugaban Chadi Idris Deby ya kwashe shekaru gommai kan karagar mulkiHoto: Getty Images/AFP/J. Demarthon

A karshen makon da ya gabata aka gudanar da zabuka a kasashen Chadi da Jibuti, ko da yake ba abu ne da ya dauki hankalin duniya sosai ba amma kasashen biyu sun ba da misali ga mai kaunar tsarin demokradiyyar yamma da wanda ke biris da shi, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung. Ta ce a Jibuti shugaba mai ci Isma'il Omar Guelleh ya samu kashi 86 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada, abin da ya bashi damar lashe zaben karo na hudu a jere. Tun a 1999 yake jan ragamar mulkin kasar da ke a yankin kahon Afirka. A Chadi har yanzu ba a samu sakamakon zaben ba amma a fili yake Shugaba Idris Déby Itno wanda tun a 1990 yake jan ragamar shugabanci, zai lashe zaben. Duk da cewa ba demokradiyya tsantsa kasashen biyu suke bi amma kasashen yamma sun yi gum da bakinsu saboda abin nan da Hausawa kan ce zaman lafiya ya fi zama dan sarki.

Rashin samun barci da daddare

Za mu karkare ne dai har wayau da jaridar ta Neue Zürcher Zeitung inda ta leka birnin Legas tana mai cewa rashin samun isasshen barci a cibiyar hada-hadar kasuwancin ta Najeriya saboda kara da hayaniyar masu ibada cikin dare da ke amfani da amsa kuwa a kusan ko wane lungu na binin. Amma yanzu hukumomin birnin sun fara daukar matakan kawo karshen hanyoyin bautar na ihu da sowa ta amfani da amsa kuwa da ke hana mutane sararawa da daddare.