Zanga-zangar Togo ta dau hankalin jaridun Jamus
July 11, 2025
Ruwanda da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ke shiga tsakani, wannan shi ne taken labarin da jaridar Zeit Online ta wallafa. Jaridar ta ce ministan harkokin wajen Ruwanda Olivier Nduhungirehe da takwararsa ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango Thérèse Kayikwamba Wagner ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a makon da ya gabata a birnin Washington, a gaban sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio. Kasashen biyu sun yi alkawarin kawo karshen goyon bayan da suke bai wa mayakan sa-kai, kuma a cikin kwanaki 90 za a janye sojojin na Ruwanda daga gabashin Kwango.
A cewar bayanai dai, yarjejeniyar tana kunshe da tanade-tanade da suka shafi mutunta yankunan kan iyakar kasa da hana tashe-tashen hankula da janyewar mayaka. Babban jigon yarjejeniyar zaman lafiyan shi ne shawarar kafa tsarin tabbatar da tsaro na hadin gwiwa na din-din-din tsakanin Kinshasa da Kigali, inji ministan harkokin wajen Ruwanda. An kuma yanke shawarar karfafa hadin gwiwar tattalin arziki, gami da kamfanonin Amurka da masu zuba jari. Ministar harkokin wajen Kwango ta ce, dole ne a bi yarjejeniyar ta hanyar fara janye sojoji.
A sharhinta mai taken: Gawarwaki a cikin tafki bayan zanga-zanga a Togo, jaridar die tageszeitung cewa ta yi: Mulkin kama-karya na iyali guda a daya daga cikin kananan kasashe a yammacin Afirka ya sake korar yunkurin tabbatar da dimukuradiyya a Lome babban birnin kasar, inda mutane suka yi dandazo a kan tituna. Gwamnati, ta yi mummunan martani na rashin tausayi. Bayan zanga-zangar da aka yi ta yunkurin danne wa tare da zubar da jini a Togo, an samu rukunin farko na gawarwaki a zahiri. Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun sanar da samun gawarwakin mutane bakwai, daga magudanar ruwa da kuma tafki a Lome babban birnin kasar. Akwai mutane da dama da suka ji rauni, kuma sama da mutane 60 ne ke tsare. Gwamnati ta ce, akwai bayanan da ba gaskiya ba ne.
Mutane da yawa sun fito kan tituna a Lomé, domin nuna adawa da Shugaba Faure Gnassingbe. Hotuna da bidiyo sun nuna wasu fusatattun matasa na kona shingayen hanya, a daya bangaren uma wasu gungun 'yan banga suna jan mutane daga gidajensu zuwa kan titunan ko kuma suna dukansu har lahira. Togo ita ce kasa ta karshe a yammacin Afirka, inda mulkin kama-karya na iyali na shekarun 1960 ke ci gaba da gudana. A cikin 1967, matashin jami'i Gnassingbe Eyadema ya kwace mulki ya kafa tsarin kama-karya. Bayan mutuwarsa a shekara ta 2005, dansa Faureembroidry Gnassingbe ya zama shugaban kasa.