Jamus na son bude wa 'yan Najeriya masu neman aiki hanyar zuwa Jamus bisa doka, yayin da kuma Jamus ke neman gwamnatin Najeriya ta bada hadin kai a kwaso 'yan Najeriya da suka shiga Jamus ta barauniyar hanya
Talla
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da yake ganawa da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a Abuja, ya bayyana bukatar huldar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu, sannan ya tabo batun 'yan gudun hijira, sai dai lokacin da shugaban gwamnatin na Jamus ya isa Lagos babban birnin kasuwancin kasar ya ga yawan 'yan Najeriya da ke bukatar fita waje, kuma ya ga halin da wasu daga cikin su da aka dawo da su daga Jamus wadanda ake bai wa horon sanin makamar aiki suke ciki.
A nan shugaban gwamnatin Jamus yace Berlin na matukar maraba da 'yan Najeriya da ke da sana'o'i wadanda ke son zuwa aiki a Jamus. Yanzu haka dai a hukumance akwai 'yan Najeriya kimanin 14,000 da ke zama a Jamus suna neman mafakar siyasa, kuma gwamnatin Jamus ta shirya mayar da su Najeriya dukkaninsu. Sai dai babbar matsalar 12,500 daga cikinsu basu da wata takarda, wanda kuma hakan ke zama abu mai wuya a iya mayar da su gida.
Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ita ma ta duba ziyarar shugaban kasar Jamus a gabashin Afirka. Inda ta ce Steinmeier ya roki gafarar Tanzaniya. Shugaban kasar ta Jamus Frank-Walter Steinmeier ya nemi garar ce a lokacin ziyarar aiki da ya kai kasar Tanzaniya, inda yace ya zama wajibi Jamus ta nemi gafara saboda abin da ta aikata wa kasar a zamanin mulkin mallaka
Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta duba ziyarar Sarkin Ingila ne Sarki Charles na III a kasar Kenya wanda shi ma batun illar mulkin mallaka ya mamaye ziyarar. Jaridar ta bude labarin da cewa doguwar muhawarar 'yan Mau Mau. Sarkin Burtaniya na III, ya yi bulaguro zuwa tsohuwar kasar da suka yi wa mulkin mallaka a Kenya. Mutane da yawa a wurin suna mamakin yadda zai tunkari wannan batu? wato mummunar murkushe tawayen Mau Mau a shekarun 1950?.
Bikin nadin Sarki Charles cikin hotuna
A Birtaniya an yi bikin nadin Sarauta na farko cikin kusan shekaru 70, irin wanda aka saba a daruruwan shekarun da suka gabata.
Hoto: Dan Charity/AP/picture alliance
A hukumance
Charles ya saka Kambun Sarauta a Mujama'ar St Edward karkashin jagorancin Archbishop na Canterbury, inda ya zauna kan kujera mai shekaru 700.
An shafe fiye da shekaru 1000 ana irin wannan bikin na kasaita a Masarautar Birtaniya. Shi dai Charles na III da ke da shekaru 74 a duniya, ya kasance sarki na 40 da ya rike wanann masarauta kana shi ne mafi tsufa da ya dare kan karagar.
Hoto: Jonathan Brady/PA/REUTERS
Kambun Sarauta
Kambun Sarautar da ya kunshi zinare wanda aka saka wa Sarki Charles na III, an yi shi tun shekarar 1661. Akwai duwatsu masu daraja fiye da 400 a jikin Kambun, wanda sabon sarkin ya saka.
Hoto: Kirsty Wigglesworth/REUTERS
Karagar sarauta
Karagar sarautar na kunshe da duwatsu masu daraja da suka yi karanci, ana ajiye ta a Scotland. A kai ake nada sarakunan Scotland.
Hoto: Kirsty O'Connor/PA Wire/picture alliance
Harabar wajen bikin
Westminster Abbey, ta kasance Cocin da ake nadin Sarauta tun shekarar 1066. Fiye da baki 2,000 aka gayyata wajen nadin Sarki Charles na III a matsayin sabon sarki.
Hoto: Gareth Cattermole/Getty Images
Sarauniya
Za a kira matar Sarki Charles na III da sunan Sarauniya Camilla a hukumance. Wannan mukamin bai sauya ba, cikin shekarun da suka gabata. Amma wasu na kiran Camilla a matsayin daya matar, saboda matar sarkin ta farko ita ce marigayiya Gimbiya Diana. Sai dai ita Camilla ta saka Kambun Sarauta wanda bai janyo cece-kuce ba.
Hoto: Gareth Cattermole/REUTERS
Barandar Fadar Buckingham
Sabon sarki da sarauniya sun koma Fadar Buckingham bayan bikin nadin Sarautar, inda suka bayyana a saman barandar fadar da sauran 'yan gidan sarautar domin gaisuwa ga dubban mutane. Yarima Andrew kani ga Sarki Charles na III da Yarima Harry karamin dan sabon sarkin, ba sa cikin wadanda suka tsaya a barandar.
Hoto: Leon Neal/AP Photo/picture alliance
Tsatson Sarauta
Yarima William wanda yake kan layin zama sarki na gaba, ya sumbaci mahaifinsa tare da durkusa a gabansa domin yin mubaya'a. William yana da yara uku, wadanda sune na biyu da na uku da kuma na hudu a layin gadon sarautar.
Hoto: Yui Mok/AP Photo/picture alliance
Wakili na wucin gadi
Kanin Yarima William wato Harry ya iso wajen bikin shi kadai, maimakon yadda ya saba zuwa tare da matarsa Meghan da ke takun saka da jaridun Birtaniya. Ba ta zo ba saboda ta tsaya agidansu na California a Amirka, domin bikin zagayowar ranar haihuwar dansu na farko Archie da ya cika shekaru hudu a ranar. Harry ya tsaya lokacin da Sarki Charles na III da sauran 'yan Sarauta suka yi faretin sojoji.
Hoto: Andy Stenning/REUTERS
Dan Uwa
An mayar da Yarima Andrew kani ga Sarki Charles na III gefe guda, tun lokacin da aka samu abokinsa Jeffrey Epstein da laifin mai dangantaka da lalata. Mai shekaru 63 a duniya shi ma an zarge shi da lalata, abin da aka sasanta a wajen kotu. Mutane sun yi wa Andrew ihu lokacin da yake wucewa.
Hoto: Roland Hoskins/AP/picture allaince
Manya
Liz Truss ta kasance firaminista ta karshe lokacin Marigayiya Sarauniya Elizabeth kana ta farko lokacin Sarki Charles na III, kuma tana cikin wadanda suka halarci bikin. Boris Johnson kuwa shi ne firaministan da ya ajiye mukaminsa a makonnin karshe na Sarauniya Elizabeth ta II.
Hoto: Gareth Cattermole/AP Photo/picture alliance
Magoya baya
Dubban mutane sun halarci bikin domin taya Charles murna, inda wasu masu goyon bayan Sarauta suka kafa sansani na kwanaki domin ganin komai kai tsaye. Mutane suna taken "Allah taimaki sarki" sannan suna rike da tutocin kasar, akwai kuma kimanin sojoji 7,000 a fadar Buckingham.
Hoto: Bruce Adams/AP Photo/picture alliance
Masu adawa da tsrain Sarauta
Ba kowa yake goyon bayan tsarin Sarauta a Birtaniya ba. Akwai masu adawa da tsarin da suke taken neman soke shi. Suna neman ganin samun tsarin zaben shugaban kasa maimakon amfani da tsarin Sarauta.
Hoto: Piroschka van de Wouw/AP/picture alliance
'Yan Sanda
'Yan sandan birnin London sun kama masu zanga-zanga da dama, inda daruruwan mutane suka fito da rubuce-rubuce lokacin bikin na ranar Lahadi. Gwamnatin Birtaniya tun farkon mako, ta kafa sabuwar dokar hana zanga-zanga.
Hoto: Scot Garfitt/AP Photo/picture alliance
Hotuna 131 | 13
A wani labarin jaridar die tageszeitung ta duba halin da ake ciki a kasar Sudan, tana mai cewa dakarun RSF sun kwace birane da dama daga hannun sojojin gwamnati. Jaridar ta kara da cewa daga cikin nasarar da RSF ta yi har da kwace biranen da ke zama hedikwatar lardi da wani muhimmin yanki da ke da rijiyaoyin mai wadanda duk suka fada hannun masu adawa da gwamnatin Sudan.
Daya daga cikin babban birnin yankin da suka kwace har da Nyala, babban birnin yankin Darfur kuma nan ne mahaifar jagioran mayakan na RSF wato Mohammed Hamdan Daglo wanda aka sani da Hemidti. Baya ga Nyala haka kuma sun kwace Zalingei, da ke babban birnin jihar Darfur.