1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Charles Konnan Bany

November 9, 2006

Praministan riƙwan ƙwaryar Cote d´Ivoire, Charles Konnan Bany, ya gabatar da jawabin farko, tun bayan hukunci da komitin sulhu na MDD ya yanke, wanda ya bashi yuƙa da nama, wajen shirye-shiryen zaɓɓuɓuka daban-daban, da za a gudanar a wannan ƙasa, kamin ƙarshen watan oktober, na shekara ta 2007.

A cikinjawabin Charles Konnan Bnnay ya ce a shire ya ke ya bi sau da kaffa mattakan da MDD ta shifida domin wannan buri.

Saidai tuni masu fashe bakin harakokin siyasa a Cote d´Ivoire, sunyi hasashen cewa, wanan sabuwar aniya ta Charles Konnan Banny, za ta gamu da cikas mai yawa, ta la´akari, da rashin samun cikkaken goyan baya, daga ɓangaren shugaban ƙasa Lauran Bagbo.

Kwana ɗaya kamin jawabin na Praminista, magoya bayan shugaban ƙasa, sun buƙaci, ya sauke Konnan Bany ,daga muƙamin sa.