Jawabin shekara-shekara na Georges Bush
January 24, 2007Shugaban Amurika Georges Bush, ya gabatar da jawabi ga al´umma,a game da halin da Amurika ke ciki, ta fannoni daban-daban na rayuwa.
Mahimman batutuwa guda 4 ,da ya ambato, sun haɗa da rikicin Iraki da, harakokin tsaro a cikin Amurika, kazalika George Bush, ya maida hankali a jawabin na sa a kann batun makashi da kuma baƙin haure.
A game da Iraki Bush cewa yayi:
Idan rundunar Amurika, ta hita daga Irak kamin sojojin ƙasar, su samu issashen horo ta fannin tsaro , babu shaka yan takife za su hamɓɓara da gwamnatin Irak.
Za a fuskancin haɗin gwiwa, daga ƙungiyoyin ta´ada iri 3, na farko yan schi´a, masu samun goyan baya daga Iran, sannan yan sunni, masu samun tallafi daga Alqa´ida, sai kuma yan ta´ada masu alaƙa da tsofan shugaban ƙasa.
Tashin hankalin na Irak zai ɓulla a sauran ƙasashen yankin, hakan kuwa ba ƙaramar barazana ba ce ga Amurika.