Bikin ayyana yankunan Ukraine cikin Rasha
September 30, 2022Tuni birnin Moscow ya dau haramin shagulgulan bikin, wanda a cikinsa shugaba Vladimir Poutin zai gabatar da wani kasaitaccen jawabi mai kumshe da batutuwa masu muhimmanci, in ji kakakin fadar gwamnatin Rasha Dmitri Peskov.
Rahotanni na cewa tuni Rashar ta kaddamar da wakilian gwamnatinta a yankunan Donetsk da Lougansk da Zaporijjia da Kherson da ta mamaye a Ukraine tun a ranar Alhamis, bayan tabbatar da sakamakon zaben na Raba gardama.
Kasashen yammacin duniya da dama sun yi Allah wadarai da matakin Rasha na hade yankunan a matsayin nata, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi kakkausar suka kan matakin tare da bayyana shi a matsayin wanda bai da gurbi a wannan zamani.
A nata bangare Ukraine ta bukaci kwamitin sulhu na MDD da ya yi wani zaman gaggawa a yau don duba batun.