1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin shugaban kasar Najeriya

January 8, 2012

Goodluck Jonathan ya gabatar da jawabi inda ya baiyana manufofin gwamnatinsa game da cire tallafin man fetur

Goodluck Jonathan
Goodluck JonathanHoto: AP

Shugaban Tarayya Najeriya Goodluck Jonathan ya gabatar da jawabi,game da halin da kasa ke ciki.

Shugaba ya baiyana manufofin gwamnatinsa, game da cire tallafin man fetur, wanda ya ce matakin da ya dauka tamkar abinda ya tura kusu wuta ne, ya fi wuta zafi:

"Zan iya yi amfani da wannan dama in tabatarawa 'yan Najeriya baki daya cewar, ina sane da matsanancin halin da suka shiga dalili da cire tallafin man, amma ba na yi hakan ba ne domin in kuntata masu, a' a, na aikata hakan domin shine ya fi zama alheri ga makomar kasarmu Najeriya".

Game da hare-haren da suka zama ruwan dare akasar kuwa, Goodluck Jonathan ya baiyana aniyar gwamnatinsa ta maido doka da oda cikin kasa, sannan a wani na tsimi da tanadi, shugaban ya ce gwamnati zata dauki mataki mai tsauri na zabtare albashi manyan jami'aanta, ta hanyar rage almubazaranci da kudade cikin tafiye-tafiye.

Saidai duk da jawabi na shugaban kasa, da kuma hukunci kotu na haramtawa ma'aikata gudanar ada zanga-zanga,kungiyoyin kwadagon Najeriya sun sha alwashin shiga yajin aikin sai inda mai ya kare, domin cilasta ma gwamnati ta lashe amenta.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Usman Shehu Usman

ola-sn/bds/ai t.tmf

AFP 072208 GMT JAN 12