Jawabin shugaban yan taliban Mollah Omar
November 7, 2005Talla
Tsofan shugaban kasar Afganistan Mollah Omar, da a halin yanzu, a ke kyawttata zaton ya na boye cikin tsawnuka, ya gudanar da jawabi ga daukacin musulmi na dunia, albarkacin karshen watan Ramadan.
A cikin wannan jawabi shugaban yan taliban, yayi kira ga musulmi da su yi jihadi ba ji ba gani, domin kasar Amurika ta hita daga Afganistan da Iraki, da sauran kasashen musulmi na dunia.
Mollah Omar,ya kiri musulmi da su saudakar da rayuka da dukiyoyin da su ka mallaka ga wannan jihadi, domin daukaka addininAllah.
Ya sanar cewa, za su kara matsa kaimi ga hare haren da su ke kaiwa ga Amurika, har sai ba girma ba arziki ta hita daga kasashen da ta mamaye.