JD Vance na ziyara a Hungary gabanin zaben kasar
April 7, 2026
Mataimakin shugaban Amurka JD Vance, na ziyara a Hungary, a daidai lokacin da kuri'un jin ra'ayin jama'a ke nuna alamun faduwar firaminista mai ci Viktor Orban a zaben kasar da za a gudanar a karshen wannan mako.
A al'ada dai fadar mulki ta White House ba ta tura babban jami'inta zuwa wata kasa idan ana tsaka da yakin zabe, lamarin da wasu ke tunanin ba ya rasa nasaba da alakar Shugaba Trump da da Firaminista Viktor Orban wanda ke kan gadon mulkin Hungary tun a shekaru 1990 kuma ke neman wa'adi na shida.
Amurka da Hungary sun daidaita kan makamashi
Mistar Orban dai na fuskantar hamayya mai zafi daga wani tsohon abokin tafiyarsa da ya balle daga jam'iyya mai mulki Peter Magyar, wanda kuma kuri'un jin ra'ayin jama'a ke nuna sa a kan gaba da tazara mai yawa kafin zaben Hungary na ranar Lahadi mai zuwa.