1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

JD Vance: Tattaunawa game da Greenland

Abdullahi Tanko Bala
January 14, 2026

Ministocin harkokin wajen Denmark da Greenland suna fatan kwantar da hankula a tattaunawar da za su yi a Washington kan takaddamar da ta taso game da Greenland.

Mataimakin shugaban kasar Amurka JD Vance
Mataimakin shugaban kasar Amurka JD VanceHoto: Mandel Ngan/AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kwace tsibirin na Greenland mai cin gashin kansa na kasar Denmark.

Mataimakin shugaban Amurka JD Vance zai gana ministan harkokin wajen Denmark Lokke Rasmussen da takwararsa ta Greenland Vivian Motzfeldt a Washington yayin da barazanar Trump na kwace tsibirin ke ci gaba da haifar da damuwa a Turai da kuma a tsakanin mambobin kungiyar kawancen tsaro ta NATO.

Tattaunawar wadda za ta gudana a fadar White House tare da Vance, ministan harkokin wajen Denmark ne ya bukaci hakan domin ganawa da takwaransa na Amurka Marco Rubio yana mai fatan kawar da dukkan wani shakku da kuma sabani.

Gabanin tattaunawar Firaministan Greenland Jens-Fredrik Nielsen ya ce abu guda da ya zama wajibi kowa ya fahimta shi ne Greenland ba ta bukatar zama mallaki ko kasancewa karkashin Amurka. Greenland  yanki ne mai kwaryakwaryar cin gashin kai a kasar Denmark kuma abokiyar kawancen Amurka a kungiyar tsaro ta NATO.