1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jega ya kammala wa'adinsa a INEC

Ubale Musa/PAWJune 30, 2015

A cikin alhini da rashin tabbas, shugaban Hukumar Zaben tarrayar Najeriya ta INEC ya gama aikinsa, tare da ayyana Ambasada Muhammad Wali domin jagorantar hukumar a matsayin riko.

Nigeria Wahlkommision verschiebt Wahltermin Attahiru Jega
Hoto: Stringer/AFP/Getty Images

A cikin kankanin lokaci dai ya yi nasarar kafa tarihin kasancewa mutum na farko a cikin tarihin kasar, da ya kai ga gudanar da zaben da ya kalli asarar mulki a bangaren jam'iyya mai mulki a daukacin tarihi na siyasar ta. Abun kuma da ya dauki hankali cikin kasar da ke kallon karshen wa'adin aikin Farfesa Attihiru Muhammad Jega, amma kuma babu tabbaci na makoma ga hukumar zaben da ke zaman daya a cikin cibiyoyi masu muhimmanci ga tsarin demokiradiyyar kasar mai tafiyar hawainiya.

Duk da cewar dai ya yi nasarar ambato Ambasada Mohammed Wali domin dorawa damar jagorantar INEC din zuwa samar mata magaji na hakika dai, babbar matsala na zaman makoma ta hukumar da a baya ake yiwa kallon yar amshin shata da kuma ta share shekara da shekaru tana jagorantar nadi da sunan zabe a matakai daban daban na kasar.

Jegan ya shirya zaben da ake wa kallon mafi sahihanci a tarihin kasar.Hoto: Reuters/Penney

Fargabar makomar INEC

Akwai dai tsoron mai zai faru da tsarin na'ura mai kwakwalwar da ta yi nasarar kai karshen tasirin jam'iyyar PDP na shekaru har 16, da ma inganta ragowar tsarin, da nufin kai wa ya zuwa zabe na zamanin da ke iya gamsar da masu adawa da ma masu takama da mulkin na kasa. Injiniya Buba Galadima dai na zaman jigo a cikin jam'iyyar APC mai mulki, daya kuma cikin na kan gaba ga batun sukar harkoki na hukumar can baya, kuma a tunaninsa barin na Jega na shirin bude sabon gibi a kokari na karshen matsalar zabe a kasar.

Kokarin kyautata zabe ko kuma karewar wa'adi dai tsohon malamin makaranta, kuma dan gwagwarmaya na kwadago dai ana kallon nasarar zaben kasar na watan Maris da jajircewar Jegan da ya kai ga badawa idanu toka da nufin tabbatar da sauyin da ke kama da mafarki cikin kasar.

PDP na fatan ganin hukumar ta cigaba da manufofin Jega

Duk da cewar dai ya yi nasarar kai karshen daular PDP, masu gidan na Wadata sun ce su na da sha'awar ganin magajin Jegan ya kai ga tabbatar da ingantaccen tsarin da ke iya ba kowa damar mulki cikin kasar, ko sarki ko talaka a cewar barrister Abdullahi Jalo da ke zaman mataimakin kakakin jam'iyyar na kasa.

To sai dai kuma a tunanin Ezenwa Nwagu na kungiyar Partners for Electoral Reform da ke nazarin gyara kan zaben kowa a kasar na iya rikidewa ya zuwa jega in har masu sana'ar labarai da kungiyoyi na farar hula zasu yi aikinsu a kansa.

Jama'a na fata wanda sabuwar gwamnatin za ta zaba zai kai labari.Hoto: picture-alliance/dpa

“Duk da abubuwan da ake kallon Jega da su a kafafen yada labarai da kungiyoyi na farar hula suka kai ga nadin Jega. Saboda haka ana bukatar irin wannan kulawa da matsin lamba ta 'yan kasa kan duk wanda ke shirin shugabantar hukumar. Dole ne kada mu kawar da idanunmu kan wannan, saboda hukumar na zaman mafi muhimmanci ga kasar, taf i babban banki na kasa, ko kuma kamfanin man NNPC a muhimmanci. In ba ka samu tsarin samar da shugabancin ka daidai ba to akwai matsala, kuma INEC ce ke da alhaki kan wannan, saboda haka dole ne masu sana'ar labarai da kungiyoyi na farar hula su cigaba da na mujiya kan INEC in ba haka ba to ana iya komawa baya”

Abun jira a gani dai na zaman zabi na shugabanci na kasar da ya ci moriyar gyaran Jegan yanzu kuma ke da alhaki na nada maso mai gado.