1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afganistan: Sababbin hare-hare

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 26, 2019

Wasu jerin hare-hare da kungiyar Taliban ta kai a wasu Larduna hudu na Afganistan, ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar shida tare da raunata wasu fararen hula.

Afghanistan Kabul Bombenanschlag
Jerin hare-hare a Afganistan sun halaka sojojiHoto: picture-alliance/AP/R. Gul

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaro ta Afganistan din ta fitar, ta nunar da cewa da sanyin safiya ne 'yan Taliban din suka kai wani hari da mota makare da bama-bamai a wani wajen binciken ababen hawa da ke arewacin Lardin Balkh tare da hallaka sojoji shida. Ma'aikatar tsaron ta kara da cewa wasu sojojin Afganistan din uku sun samu raunuka a gundumar Chimtal. Kakakin rundunar 'yan sanda a Lardin Khost da ke gabashin kasar Adel Haider ya ruwaito cewa an kai wani harin bam a kan jerin gwanono motocin jami'an tsaro a lardin tare da raunata fararen hula biyar. Wani harin ma a Lardin Ghazni da ke Arewa maso Gabashin kasar ta Afganistan ya halaka jami'an tsaro a wajen binciken ababen hawa da ke gundumar Deh Yak.