Jerin hare-hare kan farar hulan Isra'ila
August 18, 2011
Talla
Kafafen yaɗa labarai a Isra'ila sun ruwaito cewa an kai jerin hare-hare a kudancin ƙasar. Wasu mahara sun buɗe wuta kan wata bus dake dauke da fararen hula, inda aƙalla mutane biyar suka mutu wasu suka jikkata. Gidan radiyon Isra'ila ya ruwaito cewa daga nan sai musayar wuta tsakanin mahar da jami'an tsaro ya biyo baya. An kuma ji ƙaran fashewar wasu abube a birnin Beescheba. Kana gidan talabijin ɗin ƙasar yace an kaiwa wasu motocin hari, duk dai a kudancin ƙasar ta bani Yahudu ta yanken da suke iyaka da ƙasar Masar. Kawo yanzu Isra'ila ta yi zargin cewa maharan sun fito ne daga ƙasar Masar, amma gwamnan lardin da ke iyaka da Isra'ila ya musanta zargin.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu