Juyin mulki a Mali: Nasara ko akasinta?
August 20, 2020Za dai a iya cewa kasar ta Mali ta tsinci kanta cikin halin tsaka mai wuya ne, bayan da wata kungiya da ta kunshi 'yan adawa da kungiyoyin fararen hula da suka yi wa kansu lakabi da M5, suka fantsama zuwa kan tituna suna yin zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita.
Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yankin Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO, ta yi ta kai wa gauro da kai mari da nufin sulhunta rikicin, sai dai hakar kungiyar ba ta cimma ruwa ba. Masu zanga-zangar dai, sun dage kan bukatarsu ta lallai sai Shugaba Keita ya sauka daga kan karagar mulki.
Daga karshe dai Shugaba Keita ya yi murabus, sai dai har kawo yanzu yana tsare hannun sojojin da suka dare kan madafun ikon kasar. Tuni dai kungiyar Tarayyar Afirka ta sanar da sanya takunkumi ga Malin, yayin da kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAOz, suka ce Malin za ta ci gaba da zama cikin takunkumin da suka saka mata, har sai ta koma kan turbar dimukuradiyya.